Gwamnatin Kaduna ta bai wa mijin matar da aka ƙone da ranta gida, kuɗi da guraben karatun  yaransa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bai wa Aliyu, mijin matar da ta mutu bayan wasu fusatattun mutane sun ƙone ta da ranta a Marabar Jos, kyautar gida, tallafin kuɗi da kuma guraben karatu kyauta ga iyalansa.

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ne ya miƙa mukullin gidan ga Aliyu a ranar Talata a Fadar Gwamnatin jihar, inda ya bayyana cewa gwamnati na da alhakin tallafa wa iyalan da suka faɗa cikin irin waɗannan munanan hare-hare.

Tallafin ya biyo bayan mummunan lamarin da ya faru a Marabar Jos, inda wasu fusatattun mutane suka kashe matar Aliyu bisa zargin satar yara. Sai dai mijinta ya musanta zargin, yana mai cewa matarsa ba ta aikata laifin da ake zarginta da shi ba.

Hakazalika, Gwamna Uba Sani ya miƙa kyautar gida ga Sarah Achi, matar marigayi ɓen. Edwin Achi, wanda masu garkuwa da mutane suka kashe bayan sun yi garkuwa da shi tare da matarsa a Jihar Kaduna domin neman kuɗin fansa.

An sako Sarah Achi bayan ta shafe watanni uku a hannun masu garkuwa da mutanen, yayin da mijinta ya rasa ransa a lokacin da yake tsare.

Inji Gwamna Uba Sani, tallafin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin jihar na rage raɗaɗin da iyalan waɗanda rikice-rikice, hare-haren masu garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci suka shafa ke ciki, tare da nuna cewa gwamnati za ta ci gaba da tsayawa tare da waɗanda suka fuskanci irin waɗannan ibtilai.

By ukarofi

Leave a Reply