An bai wa Vozinha izinin amfani da laƙabinsa a Colo-Colo

Spread the love

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Chile (ANFP) ta amince ta bai wa mai tsaron ragar Cape Verde, Vozinha, damar sanya sunan da aka fi saninsa da shi a bayan rigarsa ta ƙungiyar Colo Colo.

Dan wasan mai shekaru 40 ya rattaba hannu kan kwantiragin watanni shida da ƙungiyar ta Chile (Liga de Primera) a ranar Litinin, bayan ya samu yabo a duniya saboda rawar da ya taka a gasar cin kofin duniya.

A bisa ƙa’idojin gasar, ya kamata ya buga wasa da sunansa na asali, wato Josimar Jose Evora Dias, kasancewar dokokin ANFP sun tanadi cewa “ba a yarda a sanya sunayen laƙabi ko na barkwanci” a jikin rigunan wasa ba.

Sai dai, ƙungiyar Colo Colo ta samu izinin ya buga wasa da sunan da ya shahara da shi.

Vozinha ya isa Santiago a ranar Lahadi inda magoya bayan ƙungiyar Colo Colo suka yi masa tarba ta musamman, sannan ya shiga atisaye tare da sababbin abokan wasansa bayan kwana biyu.

By ukarofi

Leave a Reply