ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Trabzonspor ta Turkiyya za ta tabbatar da sayen Mohamed Salah yayin da magoya bayanta suka yi masa tarba ta karamci a lokacin da ya isa Turkiyya.
ɗaruruwan magoya baya sun taru a wajen filin jirgin saman Ataturk da ke Istanbul ranar Laraba yayin da Salah ya fito sanye da kaya masu launukan Trabzonspor.
ɗan wasan gaban mai shekarA 34 ya bar Liverpool a ƙarshen kakar wasa da ta gabata bayan shekara tara a Merseyside, inda ya zura ƙwallaye 257.
Ba a tabbatar da albashin da Salah zai samu a Trabzonspor ba, amma tunda shi ɗan wasa ne mai zaman kansa, ƙungiyar Super Lig za ta iya ware wasu daga cikin kasafin ƙudinta don biyan albashinsa.
Salah, wanda ya zura ƙwallaye 50 a gasar Champions League, zai buga gasar ƙwallon ƙafa na zakarun Turai da Trabzonspor a kakar wasa mai zuwa bayan ta ƙare a matsayi na uku, maki takwas a bayan zakarun Turkiyya Galatasaray.
A ɗaya ɓangaren kuma, fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Masar, Mohamed Salah, ya kammala gwajin lafiyarsa cikin nasara tare da ƙungiyar Trabzonspor ta gasar Super Lig ta Turkiyya, lamarin da ya share fagen gabatar da shi a hukumance a matsayin sabon ɗan wasan ƙungiyar.
Kammala gwajin lafiyar shi ne babban mataki na ƙarshe a cinikin, kuma ana sa ran Trabzonspor za ta gabatar da kyaftin ɗin Masar ga magoya bayanta cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
Salah ya isa Turkiyya ne a farkon wannan makon, inda ɗaruruwan magoya bayan Trabzonspor suka tarbe shi cikin murna domin yi masa maraba a matsayin fitaccen ɗan wasan da ƙungiyar ta ɗauka.
Tsohon tauraron Liverpool mai shekaru 34 ya yi dukkan gwaje-gwajen lafiya da ake buƙata, kuma an tabbatar da cewa ya wuce su cikin nasara.
Yanzu dai ana sa ran Trabzonspor za ta sanar da kammala cinikin a hukumance bayan kammala sauran ƙananan matakan gudanarwa.
