
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam’iyyar ADC (ADC-PCC), ya bayyana ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyya mai mulki (APC) a matsayin yunƙurin tilasta amfani da jam’iyya guda da kama karya a Nijeriya acikin ‘yan siyasa da al’ummar ƙasa.
Daraktan yaɗa labaran ADC-PCC, Kola Ologbondiyan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya zargi APC da ƙoƙarin hana tsarin jam’iyya sama da guda da dimukraɗiyya ta shar’anta ta hanyar sanya wasu gwamnoni cikin kwamitin yaƙin neman zaɓenta da ba ‘yan jam’iyyar ba duk da cewa sun ƙi ficewa daga jam’iyyunsu domin shiga APC.
A cewarta, ba zai yiwu ɗan siyasa ya yi iƙirarin zama ɗan dimukraɗiyya ba ta hanyar amfani da ƙarfin mulkin ƙasa wajen tilasta wa gwamnonin jam’iyyun adawa shiga jam’iyyarsa da sanya su cikin kwamitin yaƙin neman zaɓe.
Daraktan ya ƙara da cewa, ajandar siyasar APC ita ce samar da iko a hannun mutum guda ta yadda zai riƙa yin hukunci akan ababen da wasu ma suna da ‘yanci a kai musamman a ƙasa irin Nijeriya mai amfani da salon mulkin dimukraɗiyya.
Ya bayyana cewa, ana amfani da cibiyoyin ƙasa, hukumomin tsaro da fannin shari’a wajen kasara ƙarfin ‘yan adawa, wanda hakan ya saɓa wa ƙa’idoji da sharuɗɗan ƙasar dimukraɗiyya da dokokin ƙasa.
Akan haka ne ya kirayi ‘yan Nijeriya da su ƙaurace wa abin da ya kira da “lalataccen salon siyasa”, wanda ake gudanarwa ta neman sake cin zaɓe bisa sallama walwalar ‘yan ƙasa, yana mai zargin jam’iyyar mai mulki da nuna halin ko-in-kula ga halin matsin tattali da al’umma suke fuskanta da rashin tsaro da ya addabi talakawan Nijeriya.
