Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Kotun tarayya mai zaman ta a Gusau a yau Juma’a, ta ɗaga ƙarar da Dr. Sani Abdullahi Shinkafi ya shigar, yana ƙalubalantar zaɓen fidda gwani na majalisar dattawa na Jam’iyyar APC a Zamfara ta Arewa zuwa 31 ga Agusta, 2026 domin yanke hukunci na ƙarshe.
Lauyan mai ƙara, Barr. Bello Galadi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala zaman kotun.
A cewarsa, Dr. Shinkafi ya shigar da ƙarar ne a kan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, Jam’iyyar APC, da kuma sanata mai wakiltar Zamfara ta Arewa a yanzu, Sanata Sahabi Ya’u Ƙaura.
Dr. Shinkafi yana ƙalubalantar tsarin da aka bi wajen fitar da Sanata Sahabi Ya’u a matsayin ɗan takar jam’iyyar APC na majalisar dattawa ta Zamfara ta Arewa a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a baya.
Barr. Galadi ya ce zaman na yau Juma’a an keɓe shi ne don gabatar da jawabai na ƙarshe na rubutu daga ɓangarorin biyu a cikin ƙarar.
“A yau mun gabatar da dukkan jawabai na ƙarshe na rubutu a gaban mai girma Alƙali, kuma kotun ta sanya 31 ga Agusta domin yanke hukunci na ƙarshe,” in ji shi.
Ya bayyana kyakkyawan fata cewa kotun za ta yanke hukunci a cikin nasara.
“In Sha Allahu, muna fata kotun za ta yi adalci,” in ji Galadi.
Dr. Shinkafi, wanda tsohon ɗan takar gwamnan Zamfara ne kuma fitaccen Jigo a jam’iyyar APC a jihar, yana neman kotu ta soke zaɓen fidda gwanin da ya fitar da Sanata Sahabi Ya’u Ƙaura, bisa zargin akwai rashin daidaito a tsarin.
Ɓangarorin da Shinkafi ya shigar da ƙara a kansu su ne INEC, APC, da Sanata Sahabi Ya’u Ƙaura.
Rahoton Blueprint Manhaja ya bayyana cewa, bayan an kammala gabatar da jawabai na ƙarshe, ɓangarorin biyu yanzu za su jira hukuncin kotu a ranar 31 ga Agusta, wanda ake sa ran zai ƙayyade wanda zai zama halastaccen ɗan takarar APC na majalisar dattawa ta Zamfara ta Arewa.
