Hukumar KASSAROTA ta cigaba da ziyarar ofishoshin ta a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hukumar kula da tsaro da zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar Katsina, KASSAROTA, ta ci gaba da rangadin duba ayyukan hukumar a ƙananan hukumomin shiyyar Daura, inda ta kai ziyara ƙananan hukumomin Dutsi da Ingawa.

Tawagar, wadda shugaban hukumar gudanarwar KASSAROTA, tsohon mataimakin Sufeto-Janar na ’yan sanda, AIG Danlami Yar’adua ya jagoranta, ta gana da hakimai, shugabannin ƙananan hukumomi, jami’an ’yan sanda masu kula da sassan, DPOs, da jami’an hukumar tsaro da kare fararen hula ta Najeriya, NSCDC, a ƙananan hukumomin.

Da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki,a ƙananan hukumomin,shugaban hukumar ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce duba yanayin aikin jami’an KASSAROTA da tantance irin alaƙar da hukumar ke da ita da sauran hukumomin tsaro, da kuma samun bayanai kai tsaye daga masu ruwa da tsaki game da ƙorafe-ƙorafe, shawarwari da ra’ayoyin da za su taimaka wajen inganta ayyukan hukumar.

AIG Danlami Yar’adua mai ritaya, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su ci gaba da bai wa jami’an KASSAROTA haɗin kai da goyon baya, domin hukumar ta samu damar cimma manufofin da aka kafa ta domin su.

A yayin ziyarar, darakta-janar na KASSAROTA, Manjo Garba Yahaya Rimi mai ritaya, yayi wa jami’an ƙananan hukumomin bayani kan nauyin da ke rataye a wuyan hukumar da hanyoyin gudanar da ayyukanta da kuma dokokin da ke jagorantar aikinta.

Ya buƙaci ƙananan hukumomin da su ci gaba da tallafawa jami’an KASSAROTA domin tabbatar da ingantaccen aikin hukumar da kyakkyawan hidima ga jama’a.

A nasu ɓangaren, hakiman gundumomi da shugabannin ƙananan hukumomin da baturen ‘yan sanda da kuma jami’an tsaro na Civil Defence na ƙananan hukumomin biyu, sun yaba wa hukumar gudanarwar KASSAROTA bisa wannan ziyara, inda suka bayyana ta a matsayin wani muhimmin mataki na ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin KASSAROTA da sauran hukumomin da ke da muhimmiyar rawar takawa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Sun kuma yaba wa ƙoƙarin hukumar na inganta tsarin zirga-zirgar ababen hawa da tabbatar da tsaron hanyoyi a faɗin Jihar Katsina, musamman a ƙananan hukumominsu, tare da ƙarfafa hukumar da ta ci gaba da wannan yunƙuri.

Sai dai masu ruwa da tsakin sun roƙi hukumar da ta ƙara yin la’akari da halin da tattalin arzikin al’umma ke ciki wajen aiwatar da dokokin zirga-zirgar ababen hawa, musamman ganin irin ƙalubalen tattalin arziki da al’ummomin karkara ke fuskanta.

Sun kuma ga hukumar da ta ƙara wayar da kan jama’a game da dokoki da nauyin da KASSAROTA ke da shi, tare da buƙatar hukumar da ta ƙara horas da jami’anta domin tabbatar da ƙwarewa, da’a da kuma kyakkyawar mu’amala da jama’a.

Tawagar da ta gudanar da rangadin ta ƙunshi mambobin hukumar Gudanarwar KASSAROTA, ciki har da tsohon kwamishinan ’yan sanda, Sulaiman Ketare da tsohon Darakta a Gwamnatin Jihar Katsina, Gambo Mashi da tsohon kwantrolan hukumar shige da fice, Dahiru Mani Bagiwa, wanda kuma yake riƙe da matsayin kwamandan KASSAROTA na Jihar.

Sauran mambobin tawagar sun haɗa da darakta-janar na hukumar, Mejo Garba Yahaya Rimi mai ritaya da sakataren hukumar, Aminu Lawal Batsari da kuma jami’in hulɗa da Jama’a na hukumar, Abubakar Marwana Kofar Sauri.

By ukarofi