Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Shugabannin gundunar ci gaban yankin Gombe South Local Council Development Area (LCDA) da ƙaramar hukumar Gombe sun ƙulla sabuwar alaƙar haɗin gwiwa da hukumar samar da Ruwa da Tsaftar Muhalli a karkara (RUWASA), domin faɗaɗa ayyukan samar da tsaftataccen ruwan sha da inganta tsaftar muhalli a yankunan.
Sabuwar haɗin gwiwar ta samu tabbaci ne yayin da tawagar RUWASA, tare da mai kula da shirin WASH na ƙaramar hukumar Gombe, suka kai ziyarar ban girma ga shugaban Gombe South LCDA, Hon. Auwal Jauro Bappi, da kuma Shugaban ƙaramar hukumar Gombe Farfesa Bappah Garkuwa.
Tawagar ta bayyana cewa manufar ziyarar ita ce taya shugabannin biyu murnar kama aiki, tare da shimfiɗa tubalin haɗin gwiwa domin bunƙasa ayyukan ruwa, tsaftar muhalli da inganta lafiyar al’umma a yankunan Gombe South da Gombe North.
A cewarsu, samar da tsaftataccen ruwan sha da inganta tsaftar muhalli na daga cikin ginshiƙan kare lafiyar jama’a, domin hakan na taimakawa wajen rage yawaitar cututtukan da ke da alaƙa da gurɓataccen ruwa da rashin tsafta.
Sun kuma bayyana cewa an tattauna hanyoyin samar da ƙarin rijiyoyin burtsatse da sauran ayyukan ruwa a unguwanni da ƙauyukan da ke fama da ƙarancin ruwa, domin tabbatar da cewa al’umma sun samu wadataccen ruwan sha mai tsafta.
Da yake jawabi, Shugaban Gombe South LCDA, Hon. Auwal Bappi, ya yaba da ziyarar tawagar RUWASA, yana mai cewa haɗin gwiwa tsakanin ƙananan hukumomi da hukumomin da ke kula da ruwa da tsaftar muhalli zai haifar da gagarumin ci gaba ga rayuwar al’umma.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga ayyukan samar da tsaftataccen ruwan sha da bunƙasa tsaftar muhalli, yana mai cewa waɗannan fannoni su ne ginshiƙan inganta lafiya da ci gaban al’umma.
Bappi ya kuma yi alƙawarin ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da RUWASA da sauran masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da cewa al’ummar Gombe South sun amfana da dukkan shirye-shiryen da gwamnati ke aiwatarwa a fannin ruwa da tsaftar muhalli.
