Saura ƙwallo 15 Ronaldo ya zura 1,000 bayan cin uku a wasan Al Nassr

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Zakaran ɗan ƙwallon ƙafar duniya Cristiano Ronaldo na gab da kaiwa matakin zura ƙwallaye 1,000 a tarihinsa na ƙwallon ƙafa bayan da ya zura na 985 a lokacin da ƙungiyarsa ta Al Nassr ta doke Al Kholood a gasar Saudi Pro League a ranar Alhamis.

Kyaftin ɗin na Portugal ya zura ƙwallaye uku ne a wasan bayan koma wa hutun rabin lokaci, wanda hakan ya sa adadin ƙwallayen nasa suka kai 985 kuma ya kusanto da shi matakin cimma gagarumar nasara a harkar ƙwallon ƙafa.

Ronaldo, mai shekaru 41 ya samu damar zura ƙwallayen ne a minti na 66, 72 da kuma 81, wanda kuma ya taimaka wa Al Nassr damar samun maki uku riris a wasan.

Haka kuma, wannan nasara ta ƙarfafa matakin ƙungiyar a Saudi Pro a matsayi na biyu, wanda ya kuma sa ta ke kai-da-kai ta fuskar maki da ta ɗaya, Al Qadsiah da ta fi ta da yawan ƙwallaye.

By Babaji

Leave a Reply