Zan iya sadaukar da raina a kan Tinubu ya ci zaɓe – Uba Sani

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa a shirye yake ya sadaukar da ransa domin Shugaba Bola Tinubu, saboda irin ayyukan raya kasa da gwamnatin tarayya ta gudanar a jihar.

Uba Sani ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin Daily Politics na Trust TV, inda ya ce goyon bayansa ga sake tsayawar Tinubu takarar shugaban kasa a 2027 ya samo asali ne daga amfanin da Kaduna ta samu, ba don wata alfarma ta kashin kansa ba.

Gwamnan ya ce Tinubu ya amince da kafa jami’o’in gwamnatin tarayya guda hudu a Kaduna, tare da sakin kuxaxe domin gyara manyan hanyoyi da kuma aikin layin dogo mai sauki.

Ya ce an kuma amince da dala miliyan 865, wato sama da naira tiriliyan 1.2, domin aikin layin dogo mai tsawon kilomita 50 daga Rigachikun zuwa Sabon Tasha.

Uba Sani ya kara da cewa gwamnatin Tinubu ta taimaka wajen samar da motocin bas masu amfani da iskar CNG guda 100 a jihar, wadanda suka yi jigilar fasinjoji sau miliyan 5.2 cikin watanni 18 da suka gabata.

Ya ce wadannan motocin sun taimaka wajen rage kudin sufuri ga ma’aikata, ‘yan kasuwa da sauran al’umma.

By ukarofi

Leave a Reply