Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Cibiyar Nazarin Manufofi da Tsare-tsaren Dabaru ta ƙasa (NIPSS), da ke Kuru a Jihar Filato, ta bayyana shirin kafa cibiyoyin horaswa guda shida a sassa daban-daban na Nijeriya. Hakan na zuwa ne yayin da masana harkokin manufofi suka nuna damuwa kan gibin da ke tsakanin horas da shugabanni da kuma ingantaccen shugabanci. Sun kuma yi kira da a sake duba tsarin shigar ɗalibai cibiyar, tsarin samar mata da kuɗaɗe da kuma aiwatar da shawarwarin manufofin da take bayarwa.
Darakta-Janar na NIPSS, Farfesa Ayo Omotayo, ne ya bayyana shirin faɗaɗa cibiyar yayin wani taron tattaunawa ta yanar gizo da ƙungiyar Nigerian Global Roundtable (NGR) ta shirya. Taron ya yi nazari kan gudummawar cibiyar ga ci gaban ƙasa tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 1979.
A cewar sanarwar da ƙungiyar mai hedikwata a ɓienna ta fitar, sabbin cibiyoyin za su faɗaɗa damar samun horaswar shugabanci tare da ƙarfafa ƙarfin NIPSS wajen bunƙasa ƙwararru a ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu. Omotayo ya tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Enugu ta riga ta ware fili domin kafa ɗaya daga cikin cibiyoyin.
Taron, wanda taken sa shi ne “Tasirin NIPSS da Gudummawarta ga Ci gaban Nijeriya”, ya samu halartar malaman jami’o’i, masana manufofin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin cibiyoyi.
A jawabinsa na maraba, Shugaban NGR kuma wanda ya shirya taron, Dakta Jones Edobor, ya yi tambaya kan ko NIPSS ta cika manufar da aka kafa ta a kai, yana mai cewa har yanzu akwai ƙarancin shugabanci nagari a fannoni daban-daban duk da shekarun da aka shafe ana horas da shugabanni.
Edobor ya tuna cewa an kafa NIPSS ne da farko domin horas da shugabannin sojoji da ma’aikatan gwamnati, kafin daga bisani a faɗaɗa shirye-shiryenta zuwa ƙwararrun ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu.
Ya bayyana cibiyar a matsayin wata muhimmiyar kafa ta ƙasa da ke nazarin manyan batutuwan da suka shafi ci gaban Nijeriya na dogon lokaci, ta hanyar tarurruka, bitoci, tarukan ƙwararru da bincike.
Sai dai ya nuna damuwa kan yadda ake ƙara kallon muƙaman shugabanci a Nijeriya a matsayin hanyar samun gata ga manyan mutane, maimakon damar yi wa al’umma hidima da sauya ƙasa zuwa mafi alheri.
“Yayin da NIPSS ke gab da cika shekaru 50 da kafuwa, wata muhimmiyar tambaya ita ce: Wane irin ci gaba cibiyar ta samu wajen cika manufar da aka kafa ta a kai?” in ji shi.
A cikin jawabinsa, Omotayo ya bayyana NIPSS a matsayin wata muhimmiyar cibiyar da ke haɗa bincike, bunƙasa shugabanci da tsara manufofi bisa sahihan bayanai da hujjoji.
Ya jaddada gudummawar cibiyar wajen inganta tsaron ƙasa, bunƙasa tattalin arziki, ƙarfafa mulkin dimokuraɗiyya da haɗin kan ƙasa, ta hanyar Babban Shirin Horas da Manyan Shugabanni (Senior Eɗecutiɓe Course — SEC) da sauran shirye-shiryenta.
Ya bayyana cewa, duk da cewa an amince da wasu shawarwarin manufofin da NIPSS ta bayar a matakin gudanar da ayyuka, har yanzu aiwatar da manyan shawarwari gaba ɗaya na fuskantar ƙalubale.
Darakta-Janar ya ce cibiyar na ba da fifiko ga nazarin abubuwan da ka iya faruwa nan gaba, domin hango sabbin barazanar tsaro da gano damar da za a iya amfani da ita wajen ci gaban ƙasa.
Omotayo ya kuma amince cewa akwai matsaloli a tsarin zaɓen waɗanda za su halarci shirye-shiryen cibiyar, yana mai cewa wasu hukumomin gwamnati kan zaɓi waɗanda za su tura ba tare da bayar da cikakkiyar dama ga NIPSS ta taka rawa a zaɓen ba.
ɗaya daga cikin manyan batutuwan da aka tattauna a taron shi ne buƙatar sake duba sharuddan shekaru da manyantaka wajen shiga Babban Shirin Horas da Manyan Shugabanni na SEC.
Mahalarta taron sun bayar da shawarar cewa bai kamata a jira sai ƙwararru sun kai wani mataki na girma a aikinsu kafin a ba su damar samun horaswar ba. Sun ce shigar da ƙwararrun ma’aikata tun da wuri zai ba su damar amfani da ilimin da suka samu wajen inganta ayyukansu na tsawon lokaci kafin ritaya.
Sun ba da shawarar fifita ’yan takarar da suka rage musu aƙalla shekaru 10 na aiki kafin ritaya. Wasu masana sun kuma ba da shawarar mayar da horaswar NIPSS cikin sharuddan samun wasu muƙaman shugabanci.
Tsohuwar Daraktar Nazari ta NIPSS, Farfesa Funmi Para-Mallam, ta yaba da gudummawar cibiyar, amma ta bayyana wasu matsalolin tsarin da suka daɗe suna kawo cikas. Waɗannan sun haɗa da siyasantar da zaɓen mahalarta, ƙarancin kuɗaɗen gudanarwa, gazawar aiwatar da shawarwarin bincike da kuma ƙarancin hulɗa da tsofaffin ɗaliban cibiyar.
Ta ba da shawarar samar da wata yarjejeniya ta musamman kan aiwatar da shawarwarin cibiyar, wadda za ta ƙarfafa gwamnati wajen ɗaukar alhakin aiwatar da manufofin da NIPSS ta gabatar.
Haka kuma, Farfesa Yusuf Adamu ya yaba wa NIPSS, amma ya yi tambaya kan ingancin yadda ake mayar da sakamakon bincike zuwa manufofin gwamnati.
Ya jaddada buƙatar samar da ingantattun dabarun sauya tsarin aiki da kuma ƙarfafa hulɗa da hukumomin da ke da alhakin aiwatar da shawarwarin.
Mahalarta taron sun ba da shawarar kafa cikakken tsarin bibiyar manufofi domin a riƙa tantance ko an amince da shawarwarin NIPSS, ko an aiwatar da su da kuma irin tasirin da suka haifar.
Sun kuma yi kira da a inganta haɗin gwiwa tsakanin cibiyar da ɓangaren zartarwa na gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu da abokan hulɗa na ƙasashen waje.
Taron ya kuma ba da shawarar gabatar da gwajin tantance ’yan takara kafin a shigar da su Babban Shirin Horas da Manyan Shugabanni na SEC, domin tabbatar da cewa ana zaɓen waɗanda suka cancanta bisa ƙwarewa da cancanta.
An kuma tattauna yiwuwar haɗin gwiwa tsakanin NIPSS da Nigerian Global Roundtable, ciki har da shirya tafiye-tafiyen nazari da sauran hulɗar ƙwararru a ƙasashen Turai.
Omotayo ya amince zai miƙa jawabin da ya gabatar ga Nigerian Global Roundtable domin wallafawa, yayin da Para-Mallam ta ɗauki alhakin gabatar da shirin ci gaba na shekaru biyar da ta tsara domin ƙarin tattaunawa.
Ana sa ran Daraktan-Janar ɗin zai yi aiki tare da Edobor da Farfesa Omonigho Otanocha na Jami’ar Man Fetur ta Tarayya da ke Warri, domin tsara yiwuwar haɗin gwiwa.
A sanarwar ƙarshe da ta fitar, Nigerian Global Roundtable ta sake jaddada muhimmancin NIPSS wajen bunƙasa shugabanci na ƙasa, inganta binciken manufofi da ƙarfafa mulkin dimokuraɗiyya.
ƙungiyar ta bayyana cewa samar da isassun kuɗaɗe masu ɗorewa, tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin shigar ɗalibai, ƙarfafa hanyoyin aiwatar da shawarwarin manufofi da kuma inganta ɗaukar alhakin gudanarwa na cibiyoyi na da muhimmanci wajen ƙara tasirin gudummawar NIPSS ga ci gaban Nijeriya.
Tattaunawar ta sake fito da babbar tambayar da aka fara da ita: Shin kusan shekaru 50 na horas da shugabanni kan dabarun tafiyar da ƙasa sun haifar da shugabanci nagari, ingantattun cibiyoyi da kuma ci gaban da za a iya aunawa a Nijeriya.
