’Yan sanda sun kama mutane 14 kan zargin jifar ayarin motocin APC a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama mutane 14 da ake zargi da hannu a harin da aka kai kan ayarin motocin magoya bayan jam’iyyar APC a kan hanyar Yashi zuwa Funtua, a ƙaramar hukumar Malumfashi.

Kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 28 ga Oktoba, 2026, da misalin ƙarfe 11 na safe, lokacin da ayarin motoci APC ke kan hanyarsu ta zuwa Funtua domin halartar ƙaddamar da toron yaƙin neman zaɓe.

Ya ce wasu da ake zargin ’yan daba ne, ɗauke da wuƙaƙe da duwatsu, sun riƙa jifan ayarin motocin da kuma motocin haya da ke wucewa, lamarin da ya haddasa farfashewar gilasan motoci da raunata mutane da dama a cikin su har akwai wasu mata.

Rundunar ta ce jami’anta sun kai ɗauki cikin gaggawa, inda suka kama mutum 14, yayin da ake ƙoƙarin cafke sauran waɗanda suka tsere.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ali Umar Fage, ya yi Allah-wadai da harin, tare da gargaɗin cewa rundunar ba za ta lamunci daba, tashin hankali ko duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya kafin zaɓe, lokacin zaɓe ko bayan zaɓe ba.

Rundunar ta tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

By ukarofi

Leave a Reply