Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa,ya ƙaddamar da sabon babban asibiti (General Hospital) na Zango, wanda shi ne babban asibiti na farko da aka taɓa kafawa a ƙaramar hukumar.
A jawabin sa, kwamishinan lafiya na Jihar Katsina, Hon. Musa Adamu Funtua, ya bayyana aikin a matsayin wani babban ci gaba a ƙoƙarin gwamnatin jihar na bunƙasa tsarin kiwon lafiya da kuma inganta samar da ayyukan kiwon lafiya ga al’umma.
Gwamnan ya bayyana cewa, an tanadi asibitin da ingantattun kayan aiki na zamani domin samar da ayyukan jinya da tiyata masu inganci, lamarin da zai rage yawan tura marasa lafiya zuwa asibitoci masu nisa tare da inganta lafiyar al’ummar Zango da maƙwabtan ƙananan hukumomi.
Ya jaddada cewa harkar lafiya na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta bai wa fifiko, inda ya lissafo muhimman nasarorin da aka samu cikin shekaru uku da suka gabata.
Nasarorin sun haɗa da ɗaga darajar cibiyoyin kiwon lafiya (CHC) guda huɗu zuwa manyan asibitoci, ci gaba da inganta wasu cibiyoyi, gyaran manyan asibitoci da ɗakunan tiyata, farfaɗo da sama da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) guda 280, ɗaukar sabbin ma’aikatan lafiya 804 aiki, gina cibiyar wankin ƙoda ta zamani (Dialysis Centre), kafa cibiyar sarrafa magunguna, da kuma faɗaɗa samar da wutar lantarki ta hasken rana a asibitocin gwamnati.
Haka kuma, Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta fara shirin horas da likitoci (Medical Residency Training) a fannoni shida na likitanci a manyan asibitocin jihar. Ya kuma bayyana cewa gwamnati na ci gaba da ɗaukar nauyin karatun ɗaliban fannin likitanci a jami’o’in cikin gida da na ƙasashen waje domin magance ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan lafiya.
Tun da farko, babban manajan hukumar kula da asibitocin Jihar, Dr. Muhammad Nazir, ya tabbatar da cewa za a gudanar da sabon asibitin cikin inganci da ƙwarewa domin samar da ayyukan lafiya ga al’umma.
A nasa jawabin godiya, shugaban ƙaramar hukumar Zango, Hon. Babangida Yardaje, ya miƙa godiyarsa ga Gwamnan bisa kafa wannan asibiti mai tarihi, tare da tabbatar masa da cewa al’ummar yankin za su ci gaba da ba da cikakken goyon baya wajen kula da kayan aikin asibitin da tabbatar da ɗorewar ayyukansa.
A ƙarshe, Gwamna Raɗɗa ya yi kira ga al’ummar ƙaramar hukumar Zango da maƙwabtan yankuna da su kare wannan katafaren asibiti tare da ba ma’aikatan lafiya cikakken haɗin kai domin tabbatar da ingantaccen aikin kula da lafiyar jama’a.
Taron ya samu halartar kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Rt. Hon Nasir Yahya Daura, shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Hon Abdulkadir Mamman Nasir, National Legal Adviser na jam’iyyar APC, Barr. Murtala Aliyu Kankia, kwamishinan yaɗa labarai, Dr. Bala Salisu Zango.
