
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis Shugaban Hukumar kula da Lamuran Tattara Kuɗaɗen shiga, Rabawa da Kasafi (RMAFC), Dakta Mohammed Bello Shehu ya ce Nijeriya ta kashe jimillar Naira tiriliyan 1.16 a tallafin fetur a shekarar 2021, kamar yadda aka zaftare tiriliyan N1.20 daga kuɗaɗen da aka samu sakamakon siyar da ɗanyen mai.
Bello Shehu ya bayyana haka ne a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Al’umma (SPAC), wanda aka ɗora wa alhakin bincike kan rahotannin kuɗaɗen masana’antar mai da gas da Shirin Masana’antun Fitarwa Na Nijeriya (NEITI) ya gudanar.
Ya ce, baya ga tallafin fetur, an yi asarar kuɗaɗen ɗanyen mai da wasu kayayyaki na jimillar Naira biliyan 16.20, N22,05 na gyaran bututu da kuma N6,75bn na kayan da suka rage.
Saidai kuma kwamitin, wanda Sanata Ibrahim Ɗankwambo ke jagoranta, ya jingine rahoton da Hukumar kula da Ci-gaban yankin Neja-Delta (NDDC) ya miƙa ga mambobi domin su yi nazari a kai tare da sake hallara a gabansa a Larabar mako na gaba.
Shugaban kwamitin ya kuma koka kan yadda Odita Janar na Ƙasa bai samu halartar zaman ba kuma ba tare da bayar da wani karɓaɓɓen uzuri ko tura wakili ba, yana mai cewa matuƙar bai je ba a Talatar mako mai zuwa, zai fuskanci ikon Majalisar Dokokin Ƙasa.
