Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samar da buhun takin zamani buhu 200,800 ga ƙananan manoma dubu 25,200 a jihohin bakwai na Arewa maso Yamma inda kowane manomi zai sami buhu huɗu kyauta.
Da yake ƙaddamar da rabon takin zamanin, gwamnan jihar Katsina wanda shine shugaban ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma Malam Dikko Raɗɗa ya yi gargaɗin karkatar da takin a lokacin rabawa ya ce dole takin ya isa ga manoman da aka tsara za su amfana.
“Muna gargaɗi kan karkatar da takin da aka bada kyauta dole ne ya isa ga manoman da za su amfana,”Inji Dikko Raɗɗa.
Ya ce ƙaddamar da wannan tallafin taki ya yi daidai da shirin shugaban ƙasa na Renewed Hope Agenda kan samar da wadataccen abinci ƙarƙashin hukumar NADF.
Gwamnan ya sanar da cewa jihar Katsina kaɗai za ta sami buhu 20,160 da manoma 5,040.
Ya bayana shirin zai taimaka wajan haɓaka noma da samar da wadataccen abinci da zai Inganta rayuwar ƙananan manoma.
Raɗɗa ya ce gwamnatin sa ta samar da raba buhu 400,000 na takin zamanin da fanfunan ban ruwa masu amfani da hasken rana da sauran kayan noma irin na zanani ga manoman fadin jihar.
Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumar NADF da gwamnatin jihohi da su haɗa hannu wajen tabbatar da ɗorewar shirin.
Babba da ƙaramin ministan noma da kuma ministan gidaje na daga cikin manyan mutanen da suka halarci bikin.
Haka kuma akwai mataimakin gwamnan jihar Jigawa da na Katsina da shugaban ƙungiyar manoma na ƙasa da kakakin majalisar dokoki jihar Katsina Rt Hon Nasiru Yahaya Daura da sauran manyan baƙi.
