An koka kan rashin halartar taron tunawa da Marigayi Mamman Shata a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Malami a jami’ar FUDMA Farfesa Bashir Aliyu sallau ya koka kan yadda mutane suka ƙaurace wa taron tunawa da Marigayi Alhaji Mamman Shata da ya gudana a Katsina.

Sallau wanda ke riƙe da sarautan Sarkin Askan Yariman Katsina wanda ya gabatar da jawabi a wajen taron ya nuna takaicin sa ganin yadda mawaƙin ya bada gudunmuwa wajen cigaban ƙasa,samar da zaman lafiya da ɗaukaka harshen Hausa a idon duniya amma mutane ƙalilan suka halarci taron.

Ya ce a shekarun baya irin wannan taron ɗimbin mutane daga sassan ƙasan suke halarta amma a cewar sa wannan karon mutane ko100 basu kai ba.

Farfesa Bashir Aliyu Sallau wanda tsohon darakta na hukumar tarihi da raya al’adu a Jihar Katsina ya sha alwashin ganin a shekara mai zuwa taron yafi haka armashi.

An gudanar da taron tunawa da marigayin tare da ƙaddamar da littafin da Ministan Gidaje Dr. Muttaka Rabe Darma ya buga a kan rayuwar Shata.

Taron ya samu halartar manya manyan malaman jami’a masana harsunan hausa da adabi, waɗanda suka ƙware wajen nazarin waƙoƙin Shata da ya yi a lokacin rayuwar sa.

Daga cikin su akwai Farfesa Aliyu Ibrahim Ƙankara, Dr. Nura Alƙali, Farfesa Sallau da dai sauran su. Sun kuma yi tambihi tare da bada tarihi akan waƙoƙin Shata da kuma wasu abubuwan al’ajabi da ya gudanar a lokacin rayuwarsa.

Kazalika, taron ya samu halartar Ministan Gidaje da raya birane na Najeriya, wanda kuma shi ne ya buga littafi da ya yi magana akan rayuwar Shata.

Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da iyalai na marigayi Alhaji Mamman Shata, daga cikin su har da matar shi Hajiya Hadiza, sai ya’ya, da jikoki da dai sauran su. Daga cikin ya’yan na marigayi Alhaji Mamman Shata akwai Alhaji Sanusi Mamman Shata kuma Khalifa na Mamman Shata.

A lokacin taron, anyi nishaɗi da waƙoƙin marigayi Alhaji Mamman Shata, sannan ɗa kuma Khalifan Mamman Shata Alhaji Sanusi Mamman Shata ya rera wasu baitoci na wasu daga cikin waƙoƙin marigayin watau Alhaji Mamman Shata Katsina.

Taron na tunawa Shatan na wannan shekara mai taken “Gudumuwar Shata domin samar da zaman lafiya, Tltsaro da kuma dimokuraɗiyya.

By ukarofi

Leave a Reply