Tsohon mataimakin gwamnan Bauchi, Sule Katagum ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Bauchi, Audu Sule Katagum ya rasu.

Sule Katagum, wanda shi ne kuma Wazirin Katagum, ya rasu ne a jiya Asabar a Asibitin Nizamiye da ke Birnin Tarayya Abuja, lamarin da ya kawo ƙarshen zangonsa na yi wa al’umma da ƙasa hidima.

Rasuwarsa ta sa jagororin siyasa daga sassa daban-daban na Bauchi sun riƙa aika saƙonnin ta’aziyya, inda da dama suka bayyana shi a matsayin jajirtaccen jagora da ya kasance mai hidimta wa al’ummarsa da ƙoƙarin tsare mutuncinsa a idonsu.

Gwamnan jihar, Bala Mohammed, ya bayyana kaɗuwarsa bisa faruwar al’amarin, inda ya ce hakan gagarumin rashi ne ga jihar Bauchi.

A wani saƙon ta’aziyya da ya fitar, Gwamna Bala Mohammed ya yaba wa marigayin a matsayinsa na mai biyayya kuma mai kishin ƙasa da ya sadaukar da rayuwarsa ga hidimar al’umma.

Marigayi Sule Katagum shi ne mataimakin gwamna a zamanin tsohon gwamnan Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar, MA.

A ƙarshe, gwamnan ya miƙa ta’azzarasa ga iyalai, ‘yan uwa da abokan arziƙi bisa babban rashin, yana mai addu’ar Allah ya jiƙan sa ya kuma gafara masa kurakuransa.

By Babaji

Leave a Reply