Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi
Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kebbi ta tura jami’an ‘yan sanda masana dabarun-yaƙi zuwa Tsamiya sakamakon farmakin da ‘yan ta’adda suka kai a garin da tsakar daren Asabar.
Yan ta’addan sun dira a yanki suna ta harbe-harbe ba-ji-ba- gani, sannan kuma, suka cinna wuta akan wani shingen wucin-gadi na jami’an tsaro na sibil difens.
A wata takardar sanarwa da jami’in hulda da jama’a, SP Bashir Usman ya bayar, a Birnin Kebbi, ya ce sun kuma ƙona wani gidan karuwai na ƙauye, da kuma gidan wani mutum da ake kira Sule mai goge, sannan kuma suka ɗauki wani magidanci mai suna Alhaji Yusuf Bazamfare su kayi garkuwa da shi.
Da samun wannan rahoton, kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kebbi, bai yi wata-wata ba, ya bada umurnin a tura ƙarin jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a”,
“An fara gudanar da wani bincike mai zurfi akan lamarin, sannan kuma ana ƙara ƙaimi wurin ceto mutumin da suka ɗauka, sannan kuma a cafke waɗanda sukayi wannan aika-aikan”,
“Rundunar tana bai wa mazauna Tsamiya da kewaye tabbacin cewar za’a wanzar da bada kariya ta tsaro har a kauda fargaba tsakanin al’umma”,
“Ana shawartar jama’a cewar kada suyi fargaba, amma su kasance masu kula da sanya ido akan yadda al’amura ke tafiya”, takardar sanarwar ta ce.
