Ministan Yaɗa Labarai ya kafa Kwamitin Kare Haƙƙoƙin Nakasassu

Daga WAKILINMU

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ba da umarnin kafa wani kwamiti mai mambobi biyar domin tsara aiki da hukumar nakasassu ta ƙasa domin wayar da kan jama’a game da ‘yancin nakasassu da kuma damar da suke da a rayuwa.

Mataimaki na musamman ga ministan,
Rabiu Ibrahim ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Ministan ya bayar da wannan umarnin ne a ranar Laraba, a babban birnin tarayya Abuja, lokacin da ya karbi baƙuncin babban sakataren hukumar nakasassu na ƙasa, Dr. James Lalu, a wata ziyarar ban girma da ya kai ofishinsa.

“Daga yau, za mu kafa kwamitin da zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ku domin duba takamaiman buƙatunku domin mu taimaka muku wajen ganin kun cimma su,” in ji Idris.

Ministan ya ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ya yarda da shigo da jama’a cikin gwamnatinsa musamman wajen ba wa nakasassu dama a gwamnatinsa.

Haka nan, ya ce mutane miliyan 35 da ke fama da nakasa suna wakiltar wani muhimmin rukuni na al’umma waɗanda ke da ƙwarewa, basira, da gogewa kuma za su iya daga ƙimar Nijeriya.

A nasa jawabin, babban sakataren hukumar nakasassu, Dr. Lalu, ya ce ya je ma’aikatar ne domin neman haɗin gwiwa don wayar da kan nakasassu game da haƙƙinsu.

Dokta Lalu ya ce, nakasassu na da baiwa da har kawo yanzu ba a iya amfani da ita ba a Nijeriya, waɗanda suka haɗa da fasahohi daban-daban, cancantar ƙwarewa, da basirar da ake buƙata don ci gaban tattalin arzikin ƙasa.