Sarkin Bade, Abubakar Umar ya hori masu hali su rinƙa taimakon mabuƙata

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai Martaba Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Umar Suleiman III ya hori masu hannu da shuni da su ci gaba da taimakon mabuƙata duba da halin da ake ciki na tsadar rayuwa a ƙasar.

Sarkin ya bayyana haka ne cikin makon da ya gabata a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu.

Alhaji Abubakar Umar Suleiman ya ce a halin da ake ciki yanzu na taɓarɓarewar tattalin arziki, akwai buƙatar attajirai su da masu hali su dinga taimakon na ƙasa “domin ɗorewar zumunci da ƙaunar juna”.

Haka kuma mai martaba Sarkin Alhaji Abubakar Umar Suleiman, ya kuma jinjina wa Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni bisa ƙoƙarin da yake yi na yin adalci wa al’ummar jihar da kuma ƙoƙarin gina al’umma da samar da ayyukan more rayuwa a jihar, inda ya ce gwamnan ya cika kaso mai tsoka daga cikin alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Sarkin ya ce haƙiƙa samun gwamna irin Mai Mala Buni ba ƙaramin arziki ba ne ga al’umma.

Ya kuma yi wa gwamnan fatan alheri a madadin Masarautar Bade da al’ummar jihar Yobe baki ɗaya.

Kazalika ya yi kira ga sauran shugabannin jihar da su bai wa gwamnan haɗin kai da goyon baya don ciyar da jihar gaba, inda ya bayyana cewa “ci gaba ba ya samuwa sai da bada goyon baya da kuma shawarwari masu kyau.”

Mai Martaba Alhaji Abubakar Umar Suleiman III ya yi kira ga matasan Bade da jihar Yobe baki ɗaya da su zauna lafiya da junansu, kada su zama masu tada fitina da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Kazalika Sarkin ya yi kira ga malaman addini da su ci gaba da faɗakar da al’umma zuwa ga addinin Allah.