Yadda babban kantin ƙasar Sin da ke Abuja ya hana ‘yan Nijeriya shiga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani babban kanti na kasar China da ke Abuja ya fuskanci suka bayan da aka ce ya hana kwastomomin Nijeriya shiga shagon.

Babban kantin da ke Babbar Cibiyar Kasuwanci na ƙasar Sin, dake kan titin Umaru Musa Yar’adua a Abuja, an yaba shi a matsayin wurin da ake amfani da abinci da abin sha na ƙasar Sin.

A cikin faifan bidiyo, ana iya ganin mutumin ɗan Nijeriya da ba a san ko wanene ba yana nuna ɓacin rai da kaɗuwa yayin da aka kore shi a ƙofar babban kantin.

Rahotanni sun ce hukumar ta yi nuni da takunkumin da aka yi wa kwastomomin Nijeriya, lamarin da ya sa mutumin ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda ake nuna wariya.

A cikin bayaninsa da aka ɗauka a faifan bidiyon, mutumin ya koka da halin da ake ciki, inda ya nuna rashin jin daɗin neman wasu wuraren sayayya duk kuwa da sha’awar da yake da shi na binciken abinci da kayayyakin ƙasar Sin.

Wannan binciken ya haifar da mummunan ra’ayi a tsakanin ‘yan Nijeriya da suka bayyana manufofin babban kantin a matsayin nuna bambanci. Sun yi kira ga gwamnati da ta sa baki.