Yadda ‘yan bindiga suka kashe mutum uku, suka yi garkuwa da mutum takwas a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da sace wasu 8 a wasu hare-hare biyu a jihar Kaduna a ranakun Litinin da Talata.

An yi garkuwa da mutanen ne a Unguwan Habuja da ke unguwar Kakangi a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari a jihar, inda kuma aka ce an kashe mutane biyu.

Ƙauyen yana da tazarar kilomita uku daga garin Kakangi, inda mazauna ƙauyen suka ce harin bazata ne aka kai da yammacin ranar Talata.

A cewar wani mazaunin garin, an kashe wani mutum a daya harin da ya faru a Gonan Alhaji Muntari da ke kan hanyar Birnin-Gwari Kakangi a ranar (Litinin).

Majiyar ta ce wani mutum daya da ya samu rauni a wannan lamarin yana ci gaba da karbar magani a asibitin Jibril Mai gwari.

Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kakangi a majalisar dokokin jihar Kaduna Yahaya Salio ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ya ce har yanzu yana jiran kansilan yankin ya ba shi bayani.

“Eh, gaskiya ne an kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu. Amma ina jiran cikakken bayanin lamarin daga bakin Kansilan yankin,” inji shi.