Mabiya Shi’a a Legas sun koka da ƙasashen Yahudawa bisa kisan gilla a Falasɗinu

Daga DAUDA USMAN a Legas

‘Yan uwa Musulmi al’majiran Sheikh Ibrahim Elzakzaki mabiya Shi’a da ke Jihar Legas mazauna Unguwar Mile-12 sun koka a game da abin da yake faruwa a ƙasar Falasɗinu na kashe-kashen rayukan al’ummar Musulmi da zubar da jini tare da jikkata waɗansu waɗanda ba su san hawa ba ballantana sauka kamar yadda Malam Abdullahi Ahmed wani babban malamin Shi’a a unguwar da sauran ‘yan uwa Musulmi mabiya mazahabar Shi’a a Legas suka bayyana wa jaridar Blueprint Manhaja jim kaɗan bayan kammala taron su na walimar cin abincin ƙaramar Sallah ranar Larabar makon jiya.

Babban Shehin malami na ‘yan Shi’a a Legas Sheikh Malam Abdullahi Ahmed Unguwar Mile 12 bayan ya kammala taya Musulmin gida Nijeriya dana duniya baki ɗaya murnar shigowar watan a zumin Ramadan na bana lafiya tare da kawo ƙarshensa lami lafiya, sannan kuma ya ci gaba da yi wa al’ummar Musulmin Nijeriya addu’a tare da yi masu fatan alheri na cewar sun gudanar da ibadojin su cikin nasara kuma Allah ya sanya ibadun nasu su samu karɓuwa a wajen Ubangiji.

Sannan kuma ya ci gaba da nuna rashin jin daɗinsa game da waɗansu ƙasashen Yahudawa waɗanda suka haɗa da ƙasar Amurka Ingila, Isira’iIa, Faransa da sauran ƙasashen Yahudawa ‘yan kanzaginsu suka haɗa kawunan junansu suna cutar da ƙasar Falasɗinu ta vangaren kashe mata rayukan al’umma tare da jikkata waɗansu waɗanda ba su san hawa ba ballantana kuma sauka.

Shi ma da yake gudanar da nasa tsokacin a wajen taron walimar cin abincin sallah ƙarama a Legas ɗaya daga cikin manyan ‘yan Shi’a kuma ma’ajin ɓangaren ƙungiyar ‘yan tattasai a Kasuwar Mile 12, Alhaji Sunusi Murji’i bayan kammala isar da saƙonsa na fatan alheri ga al’ummar Musulmin Nijeriya da na duniya baki ɗaya dangane da kammala azumin watan Ramadan na wannan shekarar lafiya, shi ma ya cigaba da cewa yana mai nuna rashin jin daɗinsa dangane da faruwar wannan al’amari ya ce da fatan Allah Ubangiji ya kawo wa ƙasar Falasɗinu ɗauki dangane da wannan al’amari.