Binciken gwamnatin El-Rufai: Majalisar Kaduna ta gayyaci ma’aikatar kuɗin jihar ta bayyana gabanta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kwamitin wucin gadi na majalisar dokokin jihar Kaduna da ke binciken yadda ake tafiyar da harkokin kuxi da kadarorin jihar a ƙarƙashin tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya gayyaci kwamishinan kuɗi na jihar.

Kwamitin na binciken yadda ake sayar da kadarorin gwamnati da basussukan da gwamnati ta karva a ƙarƙashin gwamnatin El-Rufai.

Magatakardar majalisar, Sakinatu Idris, a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 22, Afrilu ta buƙaci ma’aikatar kuɗi ta bayyana a ranar Alhamis a gaban kwamitin wucin gadi da wasu takardu da suka shafi bayanan jimillar rancen da gwamnati ta karɓa tsakanin shekarar 2015 – 2023.

“Jimillar basukan da aka karɓa daga watan Mayun 2015 zuwa Mayu 2023 tare da amincewar majalisar dokokin jihar Kaduna, asusun da aka shigar da basukan a ciki da kuma cirar kudi kamar yadda sake a sashen kula da harkokin kuɗi (PFMU) da ofishin kula da basussuka (DMO).

‘Yan majalisar sun kuma buƙaci ma’aikatar kuɗi da ta ba da bayanan hanyoyin biyan kwangilolin da aka bada, takardun duk wasu kuɗaɗe da aka biya ‘yan kwangila da sayar da kadarorin gwamnati, asusun ajiyar da a ka saka kuɗaɗen da siyar da kuma yadda aka kashe kuɗaɗen.

Majalisar dai ta ce za ta gayyaci waɗanda suka yi aiki lokacin gwamnatin El-Rufai, tun daga farko har ƙarshe.

Ta ce kwamitin za ta binciki kwamishinoni, shugabannin hukumomi da wasu gaggan ‘yan gaban goshin gwamnan a lokacin wannan bincike.