‘Yan Sandan a Kano sun cika hannu da wanda ake zargi da cinna wa masallata wuta a masallaci

*Ba na badamar abin da na aikata – Wanda ake zargi

Daga Rabiu Sanusi

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Kano ƙarkƙashin jagorancin CP Muhammad Usaini Gumel, ta damƙe matashi Shafi’u Abubakar bisa zargin ƙona mutane a Masallaci.

Matashin wanda ke zaune a ƙauyen Gadan dake ƙaramar hukumar Gezawar jihar Kano, ya faɗa komar hukumar ne bisa aikata laifin cinna wa wasu masallata wuta a yayin da suke sallar Asubahi.

Rundunar ta ce yayin da suka samu kiran waya daga mabambantan mutane cewa akwai matsala a wannan yankin, wanda babu ɓata lokaci Kwamishinan ‘Yan Sandan ya bada umarni ga dakarun dake kula da yanayi na dukkan wani nau’in abu mai fashewa ƙarƙashin jagorancin CSP Haruna Isma’il da DPO na Gezawa dan bincikar lamarin.

Sanarwar ta ce da isar su gurun da abin ya faru sun yi ƙoƙari matuƙa dan fitar da jama’ar dake cikin masallacin tare da kashe wutar, wanda daga bisani suka samu tabbacin mutane 24 suka samu mummunar ƙuna.

“A cikin mutum 24 ɗin nan, 20 manya ne sai kuma yara huɗu da suka samu ƙuna sosai, dan haka an gyarzaya da su zuwa asibitin Murtala dake Kano,” inji sanarwar.

Da yake yi wa ‘yan sanda bayani, wanda ake zargin ya ce, wai mutanen unguwar tasu suna yi masa wasu maganganu da shi ba zai iya tantace abin da suke faɗa ba, kuma shi ya yi masu magana su bari ba su bari ba shi ya kai shi ɗaukar wannan matakin.

“Dukkan ‘yan unguwar nan tun daga kan manya da yaran su babu wanda ba ya yi mani irin wannan maganganun, amma ba su daina ba, shi ya sa na je na sayo fetur na N7000 suna sallah da Asuba wanda na zuba a cikin roba na watsa masu tare da ƙyasta ashana a kansu, kuma ba na da-na-sanin aikita haka..” Inji Shafi’u Abubakar.

Sai dai a cikin sanarwar Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan, SP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya ce wanda ya aikata laifin ya yi hakan ne kan matsalar rabon gado, ya kai ga irin wannan aikata laifin.

Kiyawa ya kuma tambayi wanda ya aikata laifin ko yana shan kayan maye? ya ce masa a’a, sai dai bai sani ba ko yana da (Makarai), wanda daga bisani aka tambaye shi ko yana wani da-na-sani akan abin da ya aikata ya ce, “a’a, in dai a kansu ne ba na wata nadama.”

Ya zuwa yanzu dai rundunarYan Sandan ta ce wanda ake zargin yana hannun su yayin da ake faɗaɗa bincike a kansa.