Gwamna Lawal ya yaba da ƙoƙarin sojoji wajen fatattakar ‘yan ta’adda a Zamfara

Spread the love

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya yaba wa dakarun haɗin gwiwa dangane da sabunta salon yaƙi da ‘yan fashin daji a jihar.

Sanarwa mai ɗauke da sa hannun kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ta ce, a ƙarshen makon da ya aka tura ƙarin sosjoji jihar domin ci gaba da fatattakar ‘yan ta’addan da ke addabar sassan jihar.

Sanarwar ta kuma bayyana ƙoƙarin da sojojin ke yi a wannan lokaci na murƙushe ‘yan ta’adda a matsayin matakin da ya dace a ɗauka na ganin bayana ɓata-garin a jihar Zamfara.

Sanarwar ta ce, “Aikin da sojoji ke yi a yankunan da lamarin ya shafa a Zamfara abun a yana ne, musamman idan aka yi la’akari da nasarorin da suka samu a ƙarshen mako.

“Aikin ya haifar da nasara mai ma’ana a yankunan ƙananan hukumomin Bungudu, Tsafe, Maru da kuma Zurmi, wanda hakan ya yi sanadiyar kashe gawurtaccen ɗan fashin dajin nan Abu Dan Dunkwuifa, wanda ya addabi ƙauyukan Bungudu da Maru.

“Kazalika, sosjojin sun kashe ‘yan bindiga da dama a ƙauye Magama Mai Rake cikin yankin Dansadau a Ƙaramar Hukumar Maru.

“Sun sake samun nasarar a Nasarawan Burkullu da ke yankin ƙaramar hukumar in Bukkuyum inda a na ma an kashe ‘yan ta’ada masu yawa tare da ceto mutane da dabbobin da aka yi garkuwa da su a ƙauyukan Kamaru, Tungar Rogo da Matsare,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa, Gwamna Lawal ya yi amfani da wannan dama wajen jajanta wa yankunan da hare-haren ta’addanci suka shafa a sassan jihar. Tare da cewa, gwamnati ta ba da himma wajen tabbatar da ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

By Editor