Don kare Nijeriya daga faɗawa fatara ya sa na cire tallafin fetur — Tinubu

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya jaddada cewa matakin cire tallafin fetur da gwamnatinsa ta ɗauka abu ne da ya zama wajibi don hana ƙasar faɗawa cikin fatara.

Tinubu ya bayyana haka a ne sa’ilin da yake jawabi a wajen taron tattalin arzikin duniya da ke gudana a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya a ranar Lahadi.

Ya ce akwai buƙatar cire tallafin na fetur domin sake farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

Ta bakinsa, “Ga Nijeriya, mun yi amannar haɗin gwiwar tattalin arziki da haɗa kai ya zama dole don samar da kwanciyar hankali a sauran ƙasashen duniya.

“Game da batun cire tallafin, ko shakka babu ya zama wajibi ƙasata ta yi fatara, don sake saita tattalin arziki da kuma hanyar ci gaba,” in ji Tinubu.

Tinubu ya amince da matsalar da ke tattare da matakin da ya ɗauka na yin watsi da manufar da ta bai wa ‘yan Nijeriya damar sayen mai a farashi mai rahusa tsawon shekaru, amma ya ce yana da yaƙinin hakan yana da amfani ga jama’a.

Idan za a iya tunawa, jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin Shugaban Nijeriya a watan Mayun 2023, Tinubu ya sanar da cire tallafin fetur.

Lamarin da ya yi sanadiyar tashin farashin kayayyakin masarufi da kuma tsadar rayuwa a ƙasar.