EFCC ne ko FCCPC?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Daga makon jiya zuwa wannan makon a Nijeriya sunayen hukumomi biyu na Gwamnatin Tarayya sun yi ta bayyana a labaru. Kai tsaye hukumomin sun haɗa da hukumar yaqi da cin hanci wato EFCC da hukumar kare haƙƙin masu sayan kaya wato FCCPC.

Hukumomin biyu sun bayyana a labaru ne don ayyukan da su ka gudanar a ɓangaren hurumin da ya shafi aikin su. Ga hukumar EFCC babban labarin da ya fito da sunan ta shi ne na yunƙurin cafke tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello. Ita kuma hukumar FCCPC ta dau matakan sauko da farashin kaya ne da wasu ‘yan kasuwa su ka cigaba da barin su da dan karen tsada duk da sauƙin da a ka sanu.

In ka ɗebe waɗannan biyun da nan gaba in Allah ya yarda za mu shiga hukumomin don ba da cikekken labarin abun da su ka aiwatar; za mu duba Ita ma rundunar ‘yan sanda da ta fito ƙarara ta bayyana matsayar ta kan yunƙurin da wasu ke yi na kafa ‘yan sandan jiha. Muhawarar nan ta kwan biyu da fara ta kuma har kullum a na samun bambancin ra’ayi tsakanin musamman masu kujerun siyasa ba ma irin gwamnoni a gefe guda da kuma jami’an tsaro ba ma irin ’yan sanda.

Babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun ya ce Nijeriya ba ta kai matsayin kafa rundunar ’yan sandan jiha ba.

Egbetokun ta hanyar wakili ya baiyana hakan a taron da majalisar wakilai ta shirya kan tsaro ne da ya shafi ‘yan sanda.

Matsayar rundunar ‘yan sanda ita ce lokaci bai yi na kafa ‘yan sandan jiha ba don haka ba daidai ne kenan yin hakan ba.

A nan babban sufeton ya nemi a dawo da rundunar SIBIL DIFENS da masu kare afkuwar hatsari karkashin rundunar.

Fargabar mutane da dama ita ce matuƙar a ka kafa rundunar ‘yan sandan jihar to gwamnoni za su iya amfani da su wajen zama ‘yan bangar su da za su rika amfani da su wajen cin zarafin abokan hamayyar su. Baya ga haka ma ga masu neman kawo aware ta hanyar kafa wa imma ƙasar Biyafara a yankin Ibo ko ƙasar Odudua a yankin Yarbawa.

Wato abun damuwar shi ne ‘yan sandan ka iya zama masu kare muradun wata ƙabila ko kuma wani addini. Mu tuna da yadda rundunar OMETEKUN ke gudanar da aiki a wasu jihohin Yarbawa da kafa wasu dokoki masu kare shiyya maimakon ƙasa baki ɗaya. Ba a je ko ina ba a kwanan nan wasu masu rajin kafa ƙasar Oduduwa sun kai farmaki kan sakatariyar gwamnatin jihar Oyo don yaɗa manufar su ta lalle a san cewa suna nan kuma kasancewar shugaban ƙasa mai ci yanzu Bayarbe ne bai dame su ba.

Masu son ɓallewa daga Nijeriya don kafa ƙasar Oduduwa ta Yarbawa da su ka nesanta kan su daga harin Oyo; sun rubutawa shugaba Tinubu wasiƙa don tattaunawar ɓallewa.

Banji Akintoye da Sunday Ogboho su ka sanya hannu kan wasiƙar da ke ba da wa’adin nan da wata biyu a tattauna da su don bin hanyar kafa ƙasar Oduduwa.

Duk da masu wasiƙar sun nesanta kan su daga waɗanda su ka kai farmaki kan sakatariyar jihar Oyo; sun ce su na wakiltar Yarbawa miliyan 60 da ke son ƙasar awaren.
Sun zargi Fulani da cewa sun hallaka mu su mutum dubu 26 da hakan ke cikin dalilan neman ƙasar da ta hada har da sassan jihar Delta, Kogi da Kwara.

Haƙiƙa barin irin wannan kamfen ya yi ƙarfi zai iya kawo barazana ga zaman ‘yan Nijeriya na wasu sassa a yankin kudu maso yamma kamar yanda a ke fama a yanzu a kudu maso gabar. Bai sabawa dokokin duniya wasu su nemi ɓallewa daga ƙasa don kafa ta su ƙasar ba amma a gaskiya a nan Nijeriya muradun na son zuciya ne don ƙarfafa wariya ta fuskar ƙabilanci da addini. Kuma maimakon masu wannan rajin su dau fafutukar ta su ta hanyar neman zaɓen raba-gardama sai ya zama ta ƙarfi da yaƙi da ma zubar da jini.

Ba na tsammanin akwai alƙaluma na kai tsaye da za su fito da adadin waɗanda sabuwar rundunar Biyafara ta IPOB kaɗai ta yi wa kisan gilla. Laifin waɗanda su ka kashen shi ne su ba ‘yan ƙabilar su ba ne ko kuma ba sa mara baya ga muradin su. Ba nan kaɗai illar ta tsaya ba ƙaddara ma karshe an samu nasarar kafa ƙasar ta Biyafara ko Oduduwa to wasu tsirsru ne za su hau madafun iko su yi ta ganawa sauran talakawa azaba. Za a iya samun babbar ƙabila mai rinjaye a sabuwar ƙasar ta danne haƙƙin karama ko sauran ƙananan ƙabilu. Ba wata riba ta gaskiya da za a iya cimmawa ta hanyar kafa irin waɗannan ƙasashe bisa doron ƙabilanci da bambancin addini ta hanyar son zuciya.

Kuma kafa rundunar ‘yan sandan jiha ka iya rura wutar aware ko yawn asarar rayuka ba gaira ba dalili sai zalunci.

Za mu dawo kan aiyuakan da su ka yi fice na hukumar EFCC da FCCPC.

Shugaban hukumar EFCC Olanipekun Olukoyede ya ce ya girmama tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da gaiyata a tsanake amma sai ya zulle.

Olukoyede da ke jawabi ga manema labaru a helkwatar hukumar ya ce ya gaji takardun zargin zarmiya da a ka yi wa Bellon don haka ya buga ma sa waya a mutunce don ya zo ya amsa tambayoyi amma sai ya kaucewa yin hakan.

A nan Olukoyede ya ce Bello ya yi zargin wata ‘yar siyasa ta dasa ‘yan jarida 100 a helkwatar EFCC don in ya zo su ci ma sa mutunci don haka ba zai zo ba.

Faruwar hakan ya sa jami’an hukumar su ka yi wa gidan Bello tsinke da misalin 7 na safe su 50 inda su ka samu kimanin jami’an tsaro 30 rike da bindigogi a gidan amma su ka kauce wa musayar wuta.

Can sai ga gwamnan Kogi Usman Ododo ya zo gidan inda lamari duk ya sauya.

Rahotanni sun nuna Ododo ya ɗauke Yahaya Bello ya arce da shi.

Olukoyede ya lashi takobin sai ya cafke Bello don ya fuskanci hukunci.

Lauyoyi da aqalla sun kai 500 sun yi dafifi a Kotun Ƙoli don mara baya ga tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello daga neman kamun EFCC.

Lauyoyin riƙe da kwalaye na neman EFCC ta dakatar da kama Bello don akwai umurnin kotu da ke dakatar da hakan.

A ganin lauyoyin da ba mamaki hayar su a ka ɗauka neman kama Bello tamkar raina sashen shari’a ne.

A nan lauyoyin sun buƙaci hukumar shari’a da shugaba Tinubu su sa baki don hana EFCC biris da umurnin kotun.

Hukumar yaƙi da cin hanci ta Nijeriya EFCC ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika.

EFCC ta ce ta tsare Sirika don binciken zargin badaƙala a kujerar ministan da ya riƙe zamanin tsohon shugaba Buhari.

“Ina tabbatar ma ka Sirika ya na hannun mu kuma mu na cigaba da gudanar da bincike da zai kai ga gurfanar da shi gaban kotu ” Inji kakakin hukumar EFCC Dele Oyewale.

Kakakin na EFCC ya yi ƙarin bayani kan tsare Sirika ya shafi zarge-zarge masu yawa da a ke yi ma sa na zarmiya a lokacin da ya riƙe kujerar minista na tsawon shekara 7.5.

EFCC ta dau lokaci ta na binciken Sirika da abun da a ka tabbatar ya shafi zargin yin ba daidai ba wajen kafa kamfanin jirgin saman Nijeriya NIGERIA AIR da ya zama ba jirgin sai dai wani jirgin Daular Larabawa da a ka yi haya don bikin ƙaddamarwar a daf da saukar shugaba Buhari daga mulki.

In za a tuna Hadi Sirika ya yi watsi da zargin da kwamitin majalisa ya yi ma sa cewa ya salwantar da Naira biliyan 85 kan aikin kafa kamfanin da bai zama zahiri ba “Naira biliyan 85 ai za ta sayi sabbin jirage 4 katakau don haka ba gaskiya ba ne. Abun da a ka yi kasafi bai fi biliyan 5 kuma abun da a ka saki bai fi biliyan 3 ba.”

Masu sharhi da masana shari’a na kiran binciken gaskiya don wanke marar laifi da cafke mai laifi a tsohuwar gwamnatin ta Buhari da ta yi kamfen kan yaki da almundahana.

Cikin tsoffin jami’an gwamnatin Buhari da ke shan bincike baya ga Hadi Sirika akwai tsohon gwamnan babban banki Godwin Emefiele, tsohuwar ministar jinkai Sadiya Umar Faruq, tsohon shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa duk da tuni an sake shi sai kuma labarin wasu manyan da wa imma a na binciken su a bayan fage ko tukun ba a buxe babin su ba.

Hukumar kare haƙƙin masu sayen kaya ta shiga manyan shaguna da kasuwanni a Abuja don tabbatar daidaita farashin kayan masarufi.

Wannan mataki ya biyo bayan yadda wasu ‘yan kasuwa su ka ƙi rage farashi duk da saukar tsadar canjin dala.

Kasuwanni a Nijeriya kan ƙara farashi bisa tashin dala don dogara da cewa da dala a ke shigo da muhimman kayan masarufi amma ba a faye samun rangwame don Naira ta samu tagomashi ba.

Muƙaddashin shugaban hukumar kare haƙƙin masu sayan kaya Adamu Abdullahi ya ce rashin bin doka ya ta’azzara tsakanin wasu ‘yan kasuwa masu cin ƙazamar riba.

Adamu Abdullahi ya ce sun rufe wani shago a unguwar Wuse don gano su na sayarwa mutane gurbatacciyar shinkafa “mun rufe shagon kuma mun kwashe shinkafar don ba za mu bari a riƙa cutar jama’a ba. Hakanan mun shiga wasu Kasuwanni don maganin wasu kungiyoyi da ke sanya farashin da su ka ga dama. “

Masu sayan kayan masarufi na ƙorafin sun kasa gani a ƙasa yayin da su ke samun labarin yadda farashin dala ke sauka.”

Shugaban ‘yan kasuwa na arewa reshen Abuja Alhaji Adamu Hassan ya ce za su tabbatar da bin doka da jan kunnen ‘yan kasuwa masu zarmewa amma ya ce ba za a samu nasara ba sai an zauna da ‘yan kasuwar don su ma a cikin tsada su ke rayuwa “yaya za a ce da zarar dala ta sauka sai a tilasta ‘yan kasuwa su sauke farashi yanzu ai dalar ta fara tashi. Ba zai yiwu CONSUMER su shigo da ƙarfi su sauke farashi ba don yanzu lokacin dimokraɗiyya. A soja an yi irin wannan a ka karya ‘yan kasuwa. “

A kwanakin baya hukumar kare haƙƙin ta rufe wani sashe na babbar kasuwar SAHAD a Abuja bayan samun farashin da na’ura ke caji ya sha bamban da wanda ke rubuce a jikin kayan.

Hukumar ta yi alwashin fadada samame a dukkanin biranen Nijeriya don samar da maslaha.

Hukumar ta na shirin rufe wani shagon ƙasar Sin a Abuja da rahotanni su ka nuna ya na nuna wariya ga ‘yan Nijeriya.

Shagon dai da ke hade da ɗakin sayar da abinci na harabar cibiyar bunkasa cinikaiya ta Sin a Abuja.

Hukumar ta ce ta fara ganin wasu faya-fayan bidiyo na ‘yan Nijeriya da ke zargin shagon da hana su shiga sai ‘yan ƙasar Sin.

Shugaban hukumar kare haƙƙin masu sayan kayan Adamu Abdullahi ya ce sun je shagon don bincike amma sai mata mai shagon da ma’aikata su ka rufe shagon su ka arce “don haka mu ka manna takarda a kofar shagon mu na gaiyatar su, su zo a Larabar nan don kare kan su kuma haƙiƙa in mun same su da laifi za mu rufe shagon gaba ɗaya don dokokin Nijeriya ba su amince da wariya ba”

Adamu Abdullahi ya ce dokar hukumar ta tanadi tara mai yawa kan duk wanda a ka samu da nuna wariya ga abokan ciniki.

Barista Yusuf Sallau Mutum Biyu lauya ne a Abuja da ke cewa yin sakaci da dokokin ke sa har wani daga ketare raina ‘yan ƙasa.

Shi ma ɗan kasuwa Alhaji Auwal Mbani Mbaka ya ce sashen laifin na ‘yan Nijeriya da ke bugewa da sha’awar shiga shagunan ‘yan Sin “a nan Kano fa har samun waje ya sa wani dan Sin neman kafa kamfanin sarrafa ruwan leda da ya dace a ce ‘yan kasa ke irin wannan sana’a.”

Za a jira sakamakon binciken hukumar kare haƙƙin kan shagon na Sin da ma wasu matakan na yaƙi da masu sayar da kaya da ɗan karen tsada duk da saukar dala.

Kammalawa;

Doka da oda ginshikƙai ne wajen cigaban kowace ƙasa don haka ya zama wajibi kowace hukumar gwamnati ta dage wajen gudanar da nauyin da ya rataya a wuyan ta cikin adalci da riƙon amana.