Kamfanonin waya sun nemi Tinubu ya ba su haɗin kai don tsauwala farashi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kamfanonin manyan layikan sadarwar da su ke aiki a Nijeriya, wato Glo, MTN, Airtel da 9Mobile, sun roƙi Gwamnatin Tarayya a karƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta sassauta wasu ƙa’idojin da ta saka wa kamfanonin, don ba su damar ƙara tsauwala farashin kuɗin kiran waya da na data.

A cewar kamfanonin, tsarin kula da farashin na yanzu bai dace da yanayin matsin tattalin arziki ba, don haka suke neman taimakon gwamnati, don magance ƙalubalen farashin.

Kamfanonin sadarwa guda huɗu sun ce, su kaɗai ne ba su yi ƙari kan farashinsu ba, wanda hakan ke barazana ga ɗorewar masana’antarsu da kuma yiwuwar karya ƙwarin gwiwar masu zuba jari a kamfanonin nasu.

Sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da Ƙungiyar Masu Lasisin Sadarwa Ta Nijeriya (ALTON) da Ƙungiyar Kamfanonin Sadarwa Ta Nijeriya (ATCON) suka fitar a ranar Alhamis.

A cewar sanarwar mai ɗauke da sa hannun Shugaban ALTON, Gbenga Adebayo, da shugaban ATCON, Tony Emokpere, ba a ƙara farashin kiran waya ko data ba a cikin shekaru 11 da suka gabata.

Sun danganta rashin ƙara farashin kuɗin kiran waya da na data da dokoki da ƙa’idojin da a ka gindaya, duk matsalolin da suka shafi tattalin arziki.

Sun ce, “don daidaita tsarin sadarwa, farashi na yanzu wanda bai dace da tattalin arzikin yanzu ba, yana barazana ga ɗorewar masana’antun sadarwa kuma yana iya karya gwiwar masu zuba jari.

“Duk da mummunan halin da ake ciki na tattalin arziki, masana’antar sadarwa ta kasance masana’anta ɗaya tilo da har yanzu ba ta sake nazarin tsarin farashin ayyukan waya ba a cikin shekaru 11 da suka gabata.”

Kazalika, kamfanonin sadarwa sun nuna damuwarsu kan yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa, inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan daƙile wannan matsala.

“Abubuwan da suka shafi sadarwa ba tare da wata shakka ba su na taka muhimmiyar rawa a cikin tsaron ƙasa da cigaban tattalin arzikin Nijeriya, musamman yadda a halin yanzu ƙasar na fama da ƙalubalen tsaro da yawa waɗanda ke buƙatar ɗaukar matakan gaggawa  don magance waɗannan barazanar.

“Hare-hare a kan hasumiyoyin sadarwa, turakun sadarwa da sauran muhimman abubuwa su na lalata ayyukan sadarwa tare da haifar da asarar kuɗi mai yawa ga kamfanoni. Mu na kira ga gwamnati da ta bayar da fifiko ga tsaron kayayyakin sadarwa da haɗa kai da jami’an tsaro, don inganta matakan kariya da yaƙi da ɓarna da zagon ƙasa yadda ya kamata.

“Masana’antar kuma ta na buƙatar saka hannun jari mai yawa a cikin faɗaɗa cibiyar sadarwa da haɓaka fasahar zamani,” inji su.