Da Ɗumi-ɗumi: Gwamna Obaseki ya amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a jiharsa

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Edo, Mr. Godwin Obaseki, ya yi wa ma’aikatan jihar ƙarin albashi daga N40,000 zuwa N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a wajen ƙaddamar da sakatariyar zamani na Ƙungiyar Ƙwadago a jihar a Benin City, babban birnin jihar.