An buƙaci Tinubu ya ja kunnen EFCC kan yi wa doka karan-tsaye

Daga BASHIR ISAH

An yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan ya ja kunnen Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) bisa karan-tsayen da take yi wa doka wajen gudanar da harkokinta.

An buƙaci Tinubu ya taka wa EFCCn burki ne bayan da ta yi yunƙuri cafke tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, duk da cewa a baya umarnin kotu ta haramta mata hakan.

Idan za a iya tunawa, a ranar 9 ga Fabrairu, 2024, Babbar Kotun da ke zamanta a Lokoja, ta yanke hukunci kan ƙara mai lamba HCL/68M/2024 tsakanin Alhaji Yahaya Bello da EFCC, inda ta hana hukumar ta EFCC ko waninta kamawa, ko tsarewa, ko hukunta Yahaya Bello, har sai ta saurari ƙarar da kuma yanke hukunci kan ƙwararan matakan tabbatar da ‘yancin ɗan’adam.

A ranar Laraba Hukumar EFCC ta yai dirar mikiya a yankin Wuse Zone 4, Abuja, inda Yahaya Bello ke da zama domin kama shi.

Da yake tabbatar da aukuwar hakan cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, kakakin Yahaya Bello ya ce, lamarin da mamaki ganin hukumar da ke gudana bisa jagorancin masanin doka amma kuma take bijere wa umarnin kotu ta hanyar aikata abin da kotu ta hana ta.

Sanarwar ta ce, “A ranar 17 ga Afrilun 2024 da misalin ƙarfe 9:30 na safe, wasu da suka bayyana kansu a matsayin jami’an EFCC suka isa Wuse Zone 4, inda Alhaji Yahaya Bello ke da zama don su kama shi.

“Wannan na zuwa ne duk umarnin da Babbar Kotu mai zamanta a Lokoja ta bayar a ranar 9 ga Fabrairu, 2024 a cikin ƙara mai lamba HCL/68M/2024 tsakanin Alhaji Yahaya Bello da EFCC.

“Inda kotun ta hana wa EFCC ko waninta kamawa, ko tsarewa, ko kuma hukunta Alhaji Yahaya Bello, har sai ta kammala sauraren ƙara da kuma yanke hukunci da take ci gaba da sauraren ƙarar da kuma yanke hukunci kan ƙwararan matakan tabbatar da ‘yancin ɗan’adam.

“An sanar da EFCC wannan kamar yadda doka ta tsara a ranar 12 ga Fabrairu 2024 da kuma 26 ga Fabrairu, 2024; inda EFCC ta ɗaukaka ƙara (a cikin ƙara mai lamba CA/ABJ/CV/175/2024).”

Sanarwar ta ƙara da cewa abin takaici ne hanin hukumar da ya dace ta sa a bi doka, ita ce kuma ke bijire wa doka ta hanyar ƙin bin umarnin kotu.

Don haka sanarwar ta ce ana kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ja hankalin EFCC kan rashin biyayya ga doka da take yi don amfanin fannin shari’ar ƙasar nan.