Tinubu ya ba da umarnin saka ɗaliban NOUN a tsarin NYSC

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ma’aikatar Ilimi ta Ƙasa da ta saka ɗaliban da suka kammala karatu a Jami’ar National Open University (NOUN) a tsarin yi wa ƙasa hidima da aka fi sani da NYSC a taƙaice.

Haka nan, Shugaban ya amince a lamunce wa ɗaliban da suka kammala NOUN halartar Makarantar Lauyoyi, wato Law School domin.

Tinubu ya ɗauki wannan mataki ne domin samun daidaito wajen baiwa ‘yan ƙasa damar cin gajiyar damammakin da ake da su a ƙasa.

Shugaba Tinubu ya bayyana haka yayin da yake jawabi a wajen taron bikin yaye ɗalibai karo na 13 wanda NOUN ta shirya ranar Asabar a Abuja.

Kafin wannan lokaci musamman a shekarar 2017, tsohon shugaban NOUN, Abdallah Adamu, ya shaida wa ɗaliban jami’ar cewa gana kaɗan za a saka ɗaliban jami’ar a tsarin NYSC da Makarantar Lauyoyi ta Nijeriya.

A baya, har kotu wasu ɗaliban jami’ar sun tafi inda suka shigar da ƙara kan rashin saka ɗaliban NOUN a tsarin NYSC da Makarantar Lauyoyi ta Ƙasa.