Bikin Easter: Rabaran Dakuru ya shawarci ma’aurata su mutunta juna

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya

Babban Rabaran na Cocin ECWA na 1 dake Uke a jihar Nasarawa, Rabaran Dokta Joshua Bulus Dakuru, ya bayyana wasu munanan ɗabi’u dake yin sanadin mutuwar aure da rashin zaman lafiya a auratayya da sauran su inda ya shawarci ma’aurata baki ɗaya musamman kiristoci, su riƙa guje wa waɗannan ɗabi’un.

Rabaran Dakuru ya bayyana haka ne a jawabin sa a lokacin wani taro na musamman don tunawa da mutuwa da kuma tashin Isa Almasihu daga matattu wadda aka gudanar a Cocin na ECWA na 1a Uke.

Rabaran Dakuru ya ce, waɗannan munanan ɗabi’u dake kawo matsaloli tsakanin ma’aurata sun haɗa da rashin so da ƙauna da rashin yarda da juna da son-kai da rashin tsoron Allah da girman kai da rashin biyayya da dai sauran su.

Ya ce ba shakka bincike ya nuna cewa waɗannan halaye su ne suke haifar da bala’i a zaman aure tsakanin kiristoci a rayuwar yau.

A kan haka nema Dakuru ya yi amfani da wannan dama inda ya buƙaci ma’aurata su riƙa sa Isa Almasihu a zamantakewarsu don shi ne kawai zai ba su hikima da ikon guje wa matsalolin.

Daga nan, ya karanta litafin Mata, sura 28 daga litafin Bibul inda ya tunatar da mabiyan cewa, kada su manta bikin na Easter na yin la’kari ne da kuma farin cikin mutuwa da kuma tashin Isa Almasihu daga matattu inda ya ƙalubalance su su tabbatar suna yin koyi da kyawawan halaye Yesu kamar yadda ya koyar.

Dangane da tsadar rayuwa da mawuyacin hali da ake fuskanta a yanzu a ƙasar nan, Rabaran Dakuru ya yi kira na musamman ga shugabanni a dukkan matakai su ji tsoron Allah su riƙa tallafa wa talakawa ta hanyar ƙirƙiro da shirye-shiryen da za su rage wa jama’a wahalar rayuwa.