‘Yan bindiga sun sace mutane da dama a Kaduna

Daga BASHIR ISAH

Bayanan da MANHAJA ta samu na nuni da cewa, ‘yan bindiga sun sace mutanen da ba a tantace adadinsu ba a ƙauyen Angwar Danko da ke mazaɓar Kakangicikin Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari, Jihar Kaduna.

Majiyarmu ta ce maharan masu yawan gaske sun dira ƙauyen da misalin ƙarfe 6 na yamma a ranar Laraba.

A cewar wani mazaunin yankin, ‘yan bindigar sun kaɗa kan mutanen ne zuwa dajin da ke kusa.

Ɗan majalisar juhar mai wakiltar Gundumar Kakangi, Yahaya Musa Dan Salio, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai ya ce bai kai ga samun cikakken bayani kan adadin waɗanda lamarin ya shafa ba.

Dan Salio ya nuna damuwarsa kan lamarin, yana mai cewa galibinsu mazana ne, tare da cewa mai yiwuwa a samu asarar rai.