JAMB ta ba da umarnin tsare duk iyayen da aka gani kusa da cibiyoyin CBT yayin rubuta jarrabawar UTME

Daga BASHIR ISAH

Hikumar Shirya Jarrabawar Neman Gurbin Karatu a Manyan Makarantu (JAMB) ta bai wa ɗaukacin cibiyoyin CBT umarni kan cewa, su sa a kama duk iyayen da suka gani kusa da cibiyarsu yayin rubuta jarrabawar UTME ta 2024

Hukumar ta ba da wannan umarnin ne yayin taron ƙarshe da ta yi da masu cibiyoyin CBT a ranar Laraba.

Mai magana fa yawun JAMB, Fabian Benjamin, ya ce umarnin ya zama wajibi duba da yadda wasu iyayen yara kan mamaye cibiyoyin CBT yayin rubuta jarrabawar kamar yadda aka shaida a baya.

Benjamin ya naƙalto Shugaban JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede na cewa, duk iyayen da aka kama da laifin bijire wa wannan umarni, za a tsare su sannan a hana ɗansu rubuta jarrabawar.

Oloyede ya ƙara da cewa, sun gano wasu ɓata-gari kan fake da sunan iyayen yara sannan su je cibiyoyin CBT yayin rubuta jarrabawa suna aikata ba daidai ba, lamarin da ya ce ba za a bari ya ci gaba da faruwa ba.

A ƙarshe, ya ce hukunar ta kammala shirye-shirye don gabatar da jarrabawar UTME ta 2024 wadda ake sa ran za a gudanar a cibiyoyin CBT 700 a sassan ƙasa.