Gwamnatin Jigawa za ta gudanar da shirin karantarwa na musamman makarantu 198

By Umar Akilu Majeri Dutse

Gwamnatin Jihar Jigawa tare da haɗin gwiwar kamfanin Mukaranta wanda ke samun tallafi daga kamfanin Bono Energy sun ware ƙananan hukumomi 12 daga 27 da jihar ke da su domin aiwatar da shirin kiyarwa na musamman a makarantun 198 da ke yankunan.

A halin da ake ciki, an kwashi malamai 240 waɗanda da su ne za a fara ɗabbaƙa wanna shiri na Mukaranta domin koya wa ɗalibai rubutu da karatu a matsayin gwaji a ɗaukacin ƙananan hukumomi 12 da za a fara shirin da su.

Ƙananan hukumomin da za su fara cin gajiyar shirin sun haɗa da Ringim da Kazaure da Roni da Auyo da Birnin Kudu da Sule Tankarkar da Garki da Hadejia da Gwaram da Birniwa da Gumel, sai kuma Babura.

Wakilinmu da ya halacci wajalen taron bitar da kamfanin Mukaranta da gwamnatin Jihar Jigawa suka shirya a cibiyar ilimi matakin farko ta Jihar Jigawa (SUBEB) domin wayar da kan malaman, ya zanta da ɗaya daga cikin malaman, Hindy Muhammad, inda ta shaida masa cewa shirin Mukaranta mai taken ‘Literacy 4prosperity, Hausa Literacy Pilot Programme for Jigawa State, an samar da shi ne domin ganin an koyar da ɗalibai karatu da harshen uwa.

Ta ƙara da cewa, shirin zai gudana ne na tsawon wata 18 zuwa shekaru uku a matsayin gwaji, wanda tuni aka bai wa malamai 240 horo don tabbatar da shirin ya cimma nasara.