Akwai ƙalubale sosai a cikin aikin jarida – Hajiya Larai Baba

“Ni ce mace ta farko da ta shugabanci gidan talabijin da rediyo a Jos”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Samun mace kamar Hajiya Larai Baba, wacce ta shafe tsawon shekaru tana aikin jarida, tana gwagwarmayar kawo sauyi al’umma, ba abu ne mai sauƙi ba. Saboda irin yadda ta samu gogewa tun da ƙananan shekaru, kuma ta yi aiki da ƙwararrun ýan jarida da suka kwanta dama, waɗanda suka riƙa sa ta a hanya har ta kai matsayin da a yanzu sunanta ya zama ruwan dare, musamman a cikin garin Jos da kewaye, sakamakon ayyukan da ta rika gudanarwa a tashar Unity FM da yadda ta kafa tashar har ta shahara a Nijeriya. ABBA ABUBAKAR YAKUBU ya samu zantawa da ita a gidan ta da ke layin Adebayo, don jin yadda take kallon rayuwa a yanzu bayan ta yi ritaya. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: Muna son ki gabatar mana da kanki. Wacce ce Hajiya Larai?

HAJIYA LARAI: Assalamu Alaikum. Sunana Hajiya Larai Baba. Ni ýar jarida ce, kuma ýar kasuwa, kuma ýar gwagwarmayar kare haƙƙoƙin al’umma.

Ko za ki gaya mana tarihinki a taƙaice ce?

An haife ni a Jihar Kaduna, yanzu haka shekaruna sama da 60 a duniya. Na yi karatuna na firamare a makarantar Kaduna Baptist School, sannan na yi karatuna na sakandire a Prince College of Commerce a garin Jos. Na samu digirina na farko kan aikin jarida a Jami’ar Jos.

Na fara aikin jarida a tashar rediyo da talabijin na Jihar Filato wacce aka fi sani da PRTVC tun tana sashin rediyo daban na talabijin daban. Na yi aiki a wannan tasha na tsawon shekaru 24, sai dai bayan na yi ritaya, daga bisani na samu wani aikin da kamfanin Unilever Nigeria a matsayin mai gabatar da Shirin Tallan Royco Mai Dandanon Daɗi a jihohin Kaduna, Kano, da Lagos, na tsawon shekara 6. Daga nan ne kuma na samu aiki da tashar rediyo da talabijin na Unity, inda na shafe tsawon shekara goma ina riƙe da matsayin shugabar tashar. Na yi aiki da ƙungiyoyi masu zaman kansu daban daban, waɗanda ke aiki .

Waɗanne abubuwa ne na rayuwa suka taimaka wajen mayar da ke yadda ki ka zama a yanzu?

Mu’amalata da mutane na fahimta ne, domin idan kana son jin daɗin tafiyar da al’amuranka na yau da kullum sai ka zama mai haƙuri, ladabi da biyaya ba mai girman kai ba. Waɗannan kyawawan halaye sune suka taimaka min a rayuwa na goge da rayuwa da mutane.

Kin kasance ýar jarida, ýar gwagwarmaya, ýar kasuwa, kuma uwa, wanne daga ciki ki ka fi so a riƙa ambatonki da shi?

Alhamdulillahi, kodayake ɗaya aka bani damar amsawa, amma a ra’ayina na fi son a ambace ni da duka, domin a kullum ina tare da dukkan su.

Yaya aka yi ki ka fara samun kanki a matsayin ýar jarida?

Tun ina yarinya mai shekaru biyar nake shiga zuwa gidan rediyo don shiga shirin yara da ake yi a Gidan Rediyon Jihar Kaduna, lokacin yana Nigeria Broadcasting Corporation, kafin gwamnatin tarayya ta mayar wa gwamnatin Jihar Kaduna wanda yanzu ya, ama KSMC. Tun daga nan ne na fara sha’awar zama cikakkiyar ýar jarida. Sannan har wa yau kuma mahaifiyata ta yi aiki da KSMC na tsawon shekara 35. Lokacin da ta ke wajen ina jin sha’awar magana a rediyo, kuma da na faɗa mata sai ta kaini shashin mata da yara wajen shugaban Hajiya Hassana Umar inda ta riƙa kira na Shirin Yara.

Daga nan na soma gogewa, har na kai matsayin ma gabatar da Shirin Zaben Yara. Da na shiga sakandire ma duk lokacin da muka je hutu nakan yi aikin lokacin hutu inda ake ɗan biyana, har zuwa lokacin da na kammala aka dauke artist a sashin mata da yara. Nan ma na daɗa gogewa ƙarƙashin shugaban shashin Marigariya Hajiya Salamatu Abdulkadir. Daga nan na samu kaina cikin aikin jarida.

Shin a lokacin da ki ke aiki, kin samu goyon bayan iyalinki?

Goyon baya kam Alhamdulillahi. Na gaya maka tun farko mahaifiyata ce ta fara bani ƙwarin gwiwa, shi ma kuma mijina ya bani goyon baya ɗari bisa ɗari.

Sau da dama mata ýan jarida suna kukan maza sun mamaye aikin jarida ba sa samun sakewa su yi aikin yadda ya kamata, ke yaya ki ke kallon aikin?

Ni kam na gode Allah na samu dama sosai daga wajen mazajen da muka yi aiki da su, duk da akwai matsaloli da na fuskanta. Amma yarda da Allah da jajircewa duk da yadda mazajen ke nuna rashin haɗin kai na yi haƙuri ban karaya ba, har suka haƙura, muka soma aiki da su har ma ana shawarar aiki da ni. Aikin jarida akwai ƙalubale sosai, amma da haƙuri da jajircewa aikin jarida na kowa ne, muddin akwai ilimin da kishin aikin.

Wacce gudunmawa mata ýan jarida suke bayarwa ga cigaban rayuwa, musamman ga cigaban mata da iyali?

Matan ýan jarida na ba da gudumawa sosai, domin sau tari mata na da iyali haka za su bar iyalansu su je faɗakar da ýan uwa mata, ilimantar da mata yadda rayuwa take. Babu shakka ganin mata a aikin jarida sauran mata na samun ilimin rayuwa da zamantakewa.

Kin taɓa zama Babbar Manaja da ta riƙe tashar Talabijin da rediyo ta Unity a Jos, yaya ki ka samu yanayin aikin, a matsayin ki ta shugaba kuma mace?

Ni kam Alhamdulillahi, domin kuwa har na kai wannan matsayin na manaja mace ta farko da ta rike tashar rediyo da talabijin a Jos, yarda da Allah da taimakonsa ne suka kai ni. Ina kuma ƙara godiya da taimakon da ýan uwa ýan jarida da na yi aiki da su a baya suka taimaka min wajen bani shawarwari na yadda aikin zai zo min da sauqi, kazalika nima na kan nemi shawarwari daga wajensu. Domin aikin bazan iya ni kaɗai ba, sai da taimako. A taƙaice dai na riƙe tashar Unity FM da TV, kuma na yi iya ƙoƙarin da zan iya tare da goyon bayan da taimakon sauran abokan aiki.

Wacce shawara za ki bai wa matasan ýan jarida masu tasowa, don kawo sauye sauye da za su dace da zamani?

Shawarata ga matasan mu manyan gobe shine su mayar da hankali wajen aikin jarida su yi bincike sosai su ƙara sanin wannan aiki, ladabi da biyayya ga na gaba da su. Babu raina wanda ya riga fara sanin aikin jarida. Matasa su jajirce wajen yaɗa labaran gaskiya ban da yaɗa labaran ƙarya na boge wanda ba su tabbatar da ingancin su ba wato fake news. Matasa da ku muke alfahari hakuri ya zama mana matakin samun cigaba domin matasa ku ne manyan gobe. Allah ya ƙara muku basira, da juriyar aiki.

Wanne abu ne ya taɓa faruwa da ke a dalilin aikin jarida da ba za ki taɓa mantawa ba?

Akwai lokacin da nake aikin a PBC wato Plateau Broadcasting Corporation. Ƙarƙashin Marigayi Alhaji Suleiman Adara na je jin ra’ayin jama’a don ɗauko muryoyin mutane a kan batun ma’aikatar wutar lantarki a lokacin wato NEPA sai hukumar gudanarwar NEPA suka kai ƙara wajen Kwamishinan ýan sanda.

Sai Babban Manajan mu a lokacin a lokacin Injiniya Obiora ya kira ni in kawo shirin da na yi. Ni kuma sai na gayawa wanda nake aiki a ƙarƙashinsa wato Alhaji Suleiman Adara. Babu vata lokaci ya karɓi faifan shirin nan take ya je ya ga Kwamishinan. Sai aka ce sai na je. Nan take Alhaji Suleiman Adara ya ce in dai sai an kawo ni sai dai shi a rufe shi, amma ba za a kawo ni ba. Wannan abin da ya faru da ni ba zan tava mantawa ba, saboda irin fargaba da na shiga a lokacin.

Kin taɓa samun wata karramawa ko yabo saboda gudunmawar da ki ka bayar?

Gaskiya ba zan iya ƙirga lambobin yabo na karamawa da na samu ba. Na samu karramawa ta fannin muƙamai da na samu a aiki, da mua’mala ta da jama’a da dai sauransu.

Wacce gudunmawa ki ke bayarwa a ƙungiyoyin sa kai na al’umma da ki ke ciki?

Gudumawa da nake bayarwa shine faɗakarwa ga mata kan muhimmancin zamantakewa, kasuwanci ilimi, da sauran su.

Yaya ki ke kallon tasirin irin waɗannan ƙungiyoyi na NGO ga cigaban al’umma?

Waɗannan ƙungiyoyi na da tasiri cikin al’umma kwarai da gaske domin suna taimakawa inda gwamnati ba ta iya kaiwa. Waɗannan ƙungiyoyi na ilimantar da mutanen karkara sosai, suna kai taimako na musanmman domin raya al’umma.

Bayan kin yi ritaya a aiki, kin koma kasuwanci yaya ki ka fuskanci canjin yanayin rayuwar?

Bayan ritaya da na yi da man can ni ina kasuwancina tare da aikin da nake yi, don haka bai zo min da wani matsala ba.

Yaya batun iyali?

Ina da iyali, kodayake Allah ya yi wa maigidana rasuwa shekaru goma sha biyu da suka gabata. Ina da yara huɗu maza uku mace daya. Ga kuma jikoki.

Menene burinki nan gaba a rayuwa?

Burina nan gaba shi ne, Allah ya ƙara min lafiya, zaman lafiya tare da ni da yarana, ýan uwana da mahaifiyata. Saura kuma na bar wa Allah ya yi ikon Sa.

Wanne abu ne za ki so a ce kin samu damar canzawa a rayuwar ki, idan za a sake baki dama?

Idan zan samun dama ina son in dawo da zaman lafiya kowa ya koma mu’amala da juna. Mu zama tsinsiya maɗaurinki ɗaya.

Da wanne abu ki ke so a riƙa tunawa da ke?

Mace mai haƙuri da son zaman lafiya da kishin cigaban al’umma musanmman mata, da ƙananan yara.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwar ki?

In da rai da rabo!

Na gode.

Ni ma na gode.