Da Ɗumi-ɗumi: EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo kan almundahanar N80.2bn

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Yaƙi da Rashawa (EFCC) ta ce tana neman tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, kan zargin tafka almundahanar Naira biliyan N80.2.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na soshiyal midiya da yammacin ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce, “EFCC na neman tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ruwa a jallo bisa laifuka masu alaƙa da almundahar kuɗi da ya biliyan N80.2.

“Duk wanda ke da masaniyar inda yake ya hanzarta sanar da hukumar ko kuma ofishin ‘yan sanda mafi kusa.”

Wannan na zuwa ne sa’o’i bayan da Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, SAN ya buƙaci Bellon ya miƙa kansa cikin ruwan sanyi don yin bincike a kansa.