Gwamnan Abba ya rantsar da ƙarin kwamishinoni da mashawarta

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya rantsar da ƙarin sababin kwamishinoni guda huɗu da wasu ƙarin manyan masu ba shi shawara kan harkokin gwamnatinsa a ranar Alhamis.

Kwamishinonin da rantsarwar ta shafa sun haɗa da Hon Adamu Aliyu Kibiya da zai jagoranci Ma’aikatar Kasuwanci, sai Hon Abduljabbar Umar Garko wanda aka danƙa wa Ma’aikatar Filaye da Safiyo.

Sai kuma Hon. Shehu Aliyu Yanmedi, wanda zai kula da Ma’aikatar Ayyuka na Musamman, sannan Hon Mustapha Rabiu Kwankwaso, Ma’aikatar Matasa da Wasanni.

A ɓangare masu bai wa Gwamna shawara kuwa, su takwas ne aka rantsar a ɓangarori daban-daban da kuma shugabannin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano ƙarƙashin shugabanci Farfesa Sani Lawan Manumfashi.

Haka kuma, Gwamna Kabir ya rantsar da shugabannin hukumar kula da ayyukan majalisar dokoki ta jihar Kano wadda Alhaji Gambo Sallau zai jagoranta.

Da yake jawabi, Gwamna Abba ya hori waɗanda aka rantsar ɗin su da su zamo masu gaskiya da riƙon amana tare da sadaukar da kai da jajircewa yayin gudanar da ayyukan su.

Ya kuma buƙaci al’umma da su ƙara taimaka wa gwamnatinsa da addu’o’in samun nasara da zai ba su ikon ci gaba da gudanar da ayyukan cigaban Jihar.

Bugu da ƙari, ya kuma sauya wa wasu daga cikin kwamishinonin ma’aikatu, yayin da aka ɗaga likafar wasu daga cikin masu bada shawara da daraktoci.