Duk wanda ba zai kare gwamnatin Tinubu ba ya ƙara gaba – Gargaɗin Matawalle

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya yi kakkausan gargaɗi ga ‘yan Arewa da ke cikin gwamnatin Bola Tinubu cewa duk wanda ba zai kare gwamnati ba, to ya sauka ya ƙara gaba.

“Yanzu fa ba lokacin da za a yi shiru ba ne.Tilas mu tashi tsaye a san muna cikin wannan gwamnati, ko kuma mu fice kowa ya ƙara gaba.

Matawalle ya yi wannan kakkausan furuci ne a matsayin raddi ga ɗaya daga cikin ‘yan Arewa da ke cikin gwamnatin Tinubu, wato Hakeem Baba-Ahmed.

Mashawarcin Musamman ne ga Tinubu a Harkokin Siyasa, ya shiga shafinsa na Facebook, ya ce kamata ya yi Matawalle ya fara bayyana irin ci gaban da ya samar a matsayin sa na minista, sai kuma ci gaban da sauran ‘yan Arewa da ke cikin gwamnatin suka samar, sai a auna na kowa a gani, maimakon ya fito ya na ragargazar ƙungiyar Dattawan Arewa.

A ranar Lahadi ce dai Matawalle ya ce ‘Ƙungiyar Dattawan Arewa ba da yawun Arewa suke magana ba’.

Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya ragargaji ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), dangane da wata barazana da suka yi wa Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ko kuma gwamnatin sa.

Cikin wata sanarwar da Matawalle ya fitar a ranar Asabar, tsohon gwamnan Jihar Zamfara ɗin ya ce dattawan Arewa ba da yawun ‘yan Arewa suke magana ba.

Matawalle ya ce ƙungiyar NEF gungun wasu dattawa ne kawai da suke ƙware wajen gutsiri-tsoma da tsugudidin surutan da ke zubar wa Arewa da mutunci da martabar yankin.

Ya ce idan ka ji NEF na wani ɓaɓatu, to buƙatar kan su ce ko wata manufar su suke don cimmawa.

Ya ce muguwar halayyar ƙungiyar dattawan da ke kiran kan su Dattawan Arewa ta fama gundumar kowa, ya ce ba su iya bijiro da wani kyakkyawan tunanin da zai iya kawo ci gaban Nijeriya a nan gaba ko a yanzu, ko su kawo wani tunanin da zai ƙara kawo haɗin kai tsakanin mabambantan al’ummomin cikin Nijeriya.

Ya ce ƙungiyar na yin harbin-iska ne kawai da soki-burutsu, saboda ɗan takarar su na zaɓen 2023 bai yi nasara ba.