Ana yi wa harkar rubutu shiga shantun ƙadangare – Abou Othaymeen

“Ina fatan na narka ruwan gwalagwalan hikimomin da aka yi mini baiwar sa”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Malam Nura Isma’il, wanda aka fi sani da Abou Othaymeen, ba voyayye ba ne a tsakanin marubutan adabi na Hausa da Turanci, har ma da Larabci. Ya daɗe yana ba da gudunmawa a ɓangaren adabin zube da rubutattun waƙoƙi. Sannan kuma har wa yau hafizi ne na Alƙur’ani Mai Girma, kuma malamin makaranta. Shi ne ya jagoranci tilawar haddar Alƙur’ani Mai Girma da marubuta suka gudanar a zauren marubuta na manhajar WhatsApp. A tattaunawar sa da Abba Abubakar Yakubu, Malam Nura, ya bayyana shawararsa kan yadda za a ƙara samun haɗin kai a tsakanin marubuta, da ƙalubalen rashin tsayayyun dokoki da sharuɗɗa na shigowar marubuta, kamar yadda ya ce ana yi wa harkar shiga shantun ƙadangare.

MANHAJA: Ko za ka gabatar mana da kanka?

ABU OTHAYMEEN: Sunana Nura Isma’il Abubakar, wanda aka fi sani da Abou Outhaymeen (Abu Usaimin). Marubuci kuma malamin makaranta.

Gaya mana tarihin rayuwarka a taƙaice.

An haife ni a ƙarshen ƙarni na 20 na miladiyya, a Unguwar Gama da ke Ƙaramar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano. Na fara karatun allo a makarantar Malam Isuhu Mai-Mai. Daga baya na koma makarantar Malam Sirajo (Allah Ya masa rahama amin). Daga bisani kuma na shiga makarantar firamare a Gawuna Science And Technical, sai kuma na wuce G.S.S Stadium. Bayan wasu shekaru na samu gurbi a Jami’ar Bayero, a Tsangayar Nazarin Kimiyyar Ƙasa da Muhalli. A nan na karanci ilimin Geography. Bayan kammala hidimar ƙasa, a yanzu ni malami ne a Sashen Kimiyyar Alƙur’ani da ke Kwalejin Ilimi ta Alfajr da ke nan Kano.

Ko za mu san waɗanne abubuwa ka samu zarafin gudanarwa a harkokin adabi, ko ake kan bayarwa?

Da yake ɗalibin ilimi ne ni, kusan ɓangarori uku na adabi na kewaya su. Wato adabin zube ko rubutaccen adabi da kuma adabin baka. Sai kuma nazari. Na yi rubuce-rubuce na gajeru da kuma dogayen labarai (ƙagaggu), sai kuma waqoqi da na rubuta su. Sannan kuma na yi sharhi da nazarin waƙoƙi da kuma labarai da dama. Kuma muna koyarwa tare da wayar kan marubutan da ke ƙasa da mu, gwagwardon abin da Allah Ya ƙaddara muka sanin.

Waɗanne abubuwa ne za ka iya cewa sun zaburar da kai wajen ba da lokacin ka kan rubuce-rubucen da suka shafi adabi?

To, gaskiya abubuwan da suka ingiza ni ga tsunduma a duniyar adabi ba su wuce biyu zuwa uku ba. Na farko, tasowa da sha’awar yawan karance-karance. Don tun ina ƙarami akwai yayarmu da take karanta mana littattafai kafin ta yi aure. Wannan ne ya yi mini tasiri sosai, har na fara yi da kaina. Na biyu, akwai abokaina na firamare guda biyu, waɗanda da su ne muka fara gamayyar rubutu, inda muka rubuta labarin haɗaka tun muna aji shida a firamare. Sannan sai dambarwar siyasa da ta kunno kai a shekarar 2007 wanda hakan ne ya sanya ni tilas na ɗauki alqalami na fara rubutu. Sai kuma haɗuwata da marubutan yanar gizo.

Wanne ɓangaren adabi ka fi mayar da hankali a kai, kuma ka yi rubuce-rubuce sun kai nawa?

Na fi mai da hankali a kan rubutaccen adabi musamman waƙe. Kafin na rubuta labari ɗaya, na rubuta waƙa biyar ko sama. Na rubuta dogayen labarai biyu kacal, sai gajeru sama da goma. Na yi sharhi da nazarin labarai da waƙoƙi da yawa.

Ba mu sunayen littattafai da ka yi, kawo yanzu.

Suna da yawa, akwai na Turanci, Larabci da ma Hausa. Daga ciki akwai na waƙoƙi da suka haɗa da ‘Harufan Ƙauna,’ ‘Yar Ɗagwas,’ ‘Kafiri Ne Ni,’ ‘Kar Ki Sa Hijabi,’ ‘Hausa Haiku,’ ‘Sutura Biyu,’ ‘What Should I Do?’ ‘The Rain Is Falling,’ ‘Engausa,’ ‘Ma li Araki?’ Da sauransu.

A na labaran hikaya kuma akwai, ‘I’m Going To Heaven,’ ‘Donkey’s Eve,’ ‘Kantafi,’ ‘Zakara Da Hanjin Tsumma,’ ‘Alwalar Ƙuda…’ da sauransu. Na kuma yi sharhin wasu littattafai irinsu; ‘Gwalangwaso Goma Daga Cikin Littafin Zanen Dutse,’ akwai ‘Ilimi Kyauta (Sharhin ɗaukar Jinka),’ da kuma ‘Sharhi Da Nazarin Waƙar Kas-laka,’ ‘Sharhin Waƙar Marubuta,’ da sauransu.

Idan ka waiwaya ka dubi harkokin adabi da marubuta a baya da kuma a yanzu, wanne cigaba za ka ce an samu?

Maganar gaskiya idan muka dubi saurin isar da saƙo ga al’umma, da kuma samun saduwa ta ganigaka ko ta bayan fage a kafafen sada zumunta. Lallai cigaban kamar tazarar sama da ƙasa ne. A yanzu da ka yi rubutu zai yaɗu a duniya ma, ba iya jiharka ko ƙasarka ba. Sannan ana iya cin riba tun kafin a saki labari, hallau kana iya samun masu tsaya maka ma. Kai idan rubutunka ya kai wani mataki, daga sassa daban-daban za a dinga neman ka, ana ba ka abubuwan alkairai.

Amma idan muka dubi yadda kuma kowa ke iya yi wa sabgar rubutu shiga shantun ƙadangare, lashakka rubutu ya fi daraja a baya. Don a yanzu hatta masu ci da gumin wasu sun ninku har ba adadi. Ka yi rubutu a kwafa, kuma a fi ka samun riba. Ko ka ga waɗanda suka mayar da harkar bigiren biyan buƙata suna ta hamburin hayam. Ba sa bambance halal da haram, dacewa ko akasin hakan.

Kana daga cikin shugabannin zauren Marubuta na manhajar WhatsApp, menene manufar buɗe wannan zaure, kuma shin za a iya cewa an cimma buri wajen kafuwar zauren?

Manufar shi ne samar da haɗin kai tsakanin duk marubutan Hausa ta yadda za su kasance suna da murya ɗaya da shiga sha’anin juna tamkar ‘yan’uwa. Ana son yi wa duk wani marubuci rijista ƙarƙashin ƙungiyar ta yadda za su rika magana da murya ɗaya, da tabbatar da cewa sun samu shiga cikin kowanne irin sha’ani na gwamnati da al’amuran yau da kullum. Da yi mata rijista a hukumance don samar da ma’aikata mai zaman kanta ta marubuta ko farfaɗo da ita idan akwai, domin gajiyar marubutan tare da samar da ɗa’a, da dokoki, da tsare-tsare, daidai da al’adu, addini da dokokin da ƙasa ta amince da su, domin ciyar da al’umma da qasa gaba.

Waxanne shirye-shirye na koyarwa da taimakon marubuta ake gudanarwa?

Gaskiya shirye-shiryen suna da yawa. Daga ciki dai akwai, Ina Mafita, Saki Ranka, Ƙa’idojin Rubutu, Tunaninka Kamanninka, Kiwon Lafiya, Zamantakewa, Ranar Mawaqa, Dabarun ƙirqƙirar Labari, Fatawoyin Marubuta, da sauransu. Wasu a baya aka yi su, wasu kuma yanzu ake yi.

Lokacin da al’ummar Musulmi suka gudanar da azumin Ramadan, mun ga yadda kai da wasu marubuta ku ka mayar da hankali wajen gabatar da tilawar Alƙur’ani Mai Girma, me ya kawo haka?

A bisa al’adar zauren Marubuta a duk watan Ramadana ana mayar da shirye-shiryen da ake gudanarwa zuwa na addini kai-tsaye. To, a wannan karon sai wata baiwar Allah ta ba ni shawarar me zai hana ba za a yi sauka ba! Duba da cewar akwai zauruka na marubuta da yawa da nake gudanar da abubuwan da suka shafi addini, kuma ga shi wannan wata ne na Alƙur’ani. Kai-tsaye na karvi shawararta, na kuma zaɓi Marubuta saboda shi ne babban zauren da kusan duk wani marubuci yana cikinsa. Kuma alhamdulillahi ina kai shawarar cikin marubuta, a take suka gamsu, kuma aka zartar da ita.

Yaya za ka yi bitar yadda harkokin marubuta suka gudana cikin Ramadan?

Gaskiya a ce a yi bitar Marubuta a kan abin da suka yi tsawon kwanaki 30 da wahala. Amma dai a sauƙaƙe sun yi rawar gani, wurin shiga sahun duk wani Musulmi na ƙwarai da yake mai da hankalinsa ga yawaita ibada da ambonta Allah a cikin watan Ramadana. Lallai dole a yaba wa kowa.

Waɗanne shawarwari za ka bai wa marubuta da shugabannin ƙungiyoyi wajen ɓullo da shirye-shirye irin waɗannan a zaurukansu?

Shawarar da zan ba su ita ce, ya kamata su ɗauki darasi daga abin da ya faru a wannan karon. Muna bai wa abubuwa muhimmanci ne, gwargwadon abin da muke hange za mu samu a ƙarshe. To, idan kuwa haka ne, ya muke kallon addini da lahirarmu? Ya kamata a ce komai ka ke aikatawa, a ga tasirin Musulunci a tare da kai. Domin kai wakili ne na Musulunci, kuma duk abin da ka ke yi fa, sai ka bayar da bayaninsa a gaban Mahaliccinka. Ya kamata addininka ya samu wani kaso a lokacinka, da aikinka. “Duk wanda ya shiryar a kan aikata alkairi, kamar shi ne ya aikata.”

Wacce natija aka samu daga shirin tilawar Alƙur’ani Mai Girma da aka gudanar, game da goyon bayan marubuta da haɗin kan da suka bayar?

Wallahi ba abin da za mu ce sai dai mu yi wa Allah godiya. Maza da mata kowa ya fita an yi saukar Alƙur’ani da shi. Abin da zai ba ka sha’awa marubutan da kansu suka yi, ba wai wasu aka gayyato daga waje ba. Sauka ce ta iya marubuta, su ne suka yi abinsu. Kuma wani abin burgewa! Duk wanda ya yi tuntuve tilawa ko taɗbiƙi, a take za ka ji wani ko wata sun ankarar da shi. Ma sha Allah! Wannan kaɗai ya isa zama babbar natija, domin an yi gyararraki da bayar da wasu fa’idoji da suka danganci wasu keɓaɓɓun ayoyi ko surori.

A yayin tattaunawar mu da wasu marubuta, mun ji shawarwari da aka bayar na buƙatar samar da wata babbar ƙungiya da za ta haɗo kan shugabannin ƙungiyoyin marubuta, don samar da wata Gidauniyar Tallafawa Marubuta da Mabuƙata a cikin al’umma, yaya ka ke kallon wannan shawara?

Wannan tunani ne mai kyau! Domin duk abin da za a yi shi da amo babba guda ɗaya, saqon ya fi tafiya da wuri. Hallau Musulmi ɗan’uwan Musulmi ne. Ɗan’uwa fa aka ce! Na san dai mun san ma’anar ɗan’uba. To, mu harara bambancin da ke tsakani, za mu fahimci dole rayuwa sai an dunƙule an taimaki juna.

Waɗanne hanyoyi ka ke ganin za a bi a gyara harkokin kasuwancin littattafai da bunƙasa adabi?

A cire son zuciya da son rai. Wannan shi ne abu na farko. Sannan kuma a daina tsuke abubuwa, a faɗaɗa kowa ya samu. Ina nufin a wayar da kan masu sha’awar fara ɗab’i, a nusasshe su yadda za su yi. Hakan zai sauƙaƙa al’amura sosai.

Wanne buri ka ke da shi nan gaba a matsayinka na marubuci?

“Yana ba da hikima ga wanda ya ga dama, duk wanda aka ba shi hikima, to an ba shi alheri mai yawa.”

Wannan ba kawai aya ba ce, wani azanci ne da Ubangijin gogaggun masu iya tsara zance Ya faɗa mana. Don haka ina fatan na narka ruwan gwalagwalan hikimomin da aka yi mini baiwarsa. Ya zama ruwan tawadar da alƙalamina zai ɗigar a kan takardar da tun a kallon ta, ƙwaƙwalen masu karatu za su musu fusgar maganaɗisu, su adana su domin amfani da su a rayuwarsu ta yau da gobe.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarka?

Suna da yawa, amma zan iya dunƙule su a guda ɗaya.

“Allah ɗaya, gari bamban!” Rayuwa cike take da abubuwa mabambanta, idan ka fahimci ba kai kaɗai ba ne, za ka zauna lafiya to a komai kake yi.

Na gode.

Ni ma na gode da karramawa.