Ranar Ma’aikata: Gwamnan Zamfara ya jaddada ƙudurinsa na kyautata rayuwar ma’aikatan jihar

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na kyautata wa rayuwar ma’aikatan jihar.

Ya bayyana haka ne a wajen taron bikin Ranar Ma’aikata na bana wanda aka saba gudunarwa ran 1 ga Mayun kowace shekara.

Bikin bana a jihar ya gudana ne a ranar Laraba a Sakatariyar JB Yakubu, Gusau, babban birnin jihar.

Cikin sanarwar da ta fitar, Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya ce gwamnatin jihar ba za ta baro ma’aikatan jihar a baya wajen gudanar da harkokinta.

Sulaiman ya rawaito Lawal na cewa, “Gwamnatina na sane da muhimmiyar rawar da ma’aikata ke takawa wajen tafiyar da ayyukan gwamnati. Ma’aikata da gwamnati ‘yan uwan juna ne wajen tabbatar da cigaban al’umma.

“Ma’aikata tamkar tsani ne wanda gwamnati ke amfani da shi wajen cimma manufofinta ga al’umma.

“Bisa wannan dalili ne za mu ci gaba da lalubo hanyoyin da za su amfane mu wajen kyautata rayuwarku da ta iyalanku, musamman ma a irin wannan lokaci da ake fama da tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin mai,” in ji Lawal.

By Editor