Shawara ga ‘yan uwa mata

Spread the love

Daga SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI

Assalamu alaikum. ‘Yan uwa mata barkanmu da wannan lokaci. Allah Ya shirya mana zuri’a bakiɗaya.

Zan yi amfani da wannan damar da na samu wurin yi mana tuni da kuma lurar da mu kan muhimmancin tarbiyya musamman a wannan zamanin da muka samu kanmu.


Shawarata gare mu ‘yan uwa mata dukka, duba da irin yanayin da muke ciki yanzun na taɓarɓarewar tarbiyya, ‘yan uwa mu farka daga barci, mu san ƙima da darajojin da Allah SWT yai mana ba kaɗan ba ne, mu san ciwon kanmu, mu tashi tsaye wajen ganin ɗiyanmu sun samu tarbiyya ta gari domin samun nagartacciyar rayuwa.

Mu tashi mu nemi Ilimin addini da na zamani, mu nemi sana’oi gwargwado waɗanda zasu taimaka mana mu tsaya da ƙafafunmu saboda yanayin rayuwar ta canza fiye da zatonmu.

Mu sani sai mun gyara kanmu ne za mu gyara ɗabi’un Zuriyyarmu, kasancewar mu uwaye mata ne makaranta ta farko da yaranmu ke koyon kusan dukkan darussan da za su gina rayuwarsu.

Faɗin munanan kalamai ga ɗiyanmu suna matuqar tasiri don haka muyi ƙoƙarin tsarkake harsunannmu da yin kyawawan furuci gare su, mu kasance mu kanmu muna da ɗa’a.

Janyo yaranmu a jiki na sa mu fahimci halin da suke ciki na jin daɗi ko akasin haka, ko kuma suna cikin wani yanayi da ke buƙatar ɗaukar ƙwaƙwarar mataki cikin gaggawa.

Haƙuri da juriya cikin rayuwar aurenmu gabaɗaya musamman cikin canjin yanayin rayuwar yanzun, mu kasance masu tattali da taimakon juna ta hanyoyin da suka kamata.

Taimakon waɗanda ba su kai mu wadata ba ta kowacce irin hanya domin neman lada. Rayuwar gabaɗaya sauƙi gare ta, yadda duk mutum ya ɗauke ta haka za ta kasance masa.

Uwa, uba mu dage da addu’oi ta kowanne ɓangare, ga Iyalin bakiɗaya, ga mazajenmu, ‘yan uwa, maƙwabta, shuwagabaninmu da ƙasarmu bakiɗaya.

Mu rinƙa tuna ba duniyar za mu dauwwama ba don haka mu nemi guzurin samun salama gobe ƙiyama.

Da fatan Ubangiji ya dafa mana, yaci gaba da yi mana jagoranci cikin lamurranmu bakiɗaya, ya shirya mana zuriyya bisa hanya madaidaciya, ya tsare mu da faɗawa cikin kowanne aikin zunubi ko alfahsha, ya yafe mana kura-kurenmu, ya gyara mana ƙasarmu, ya kawo mana ɗauki a Arewacin Nijeriya, ya jiƙan dukkan waɗanda suka riga mu, ya sa mu cika da Imani idan tamu ta zo.

By Editor