Ba mu wanke Betta Edu, Sadiya Farouq da wasu daga zargin harƙallar kuɗaɗe ba – EFCC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar EFCC ta bayyana cewa har yau ba ta wanke ko da mutum ɗaya da ake zargin handama, harƙalla da karkatar da kuɗaɗen Ma’aikatar Ayyukan Jinqai da Inganta Rayuwar Marasa Galihu ba.

EFCC ta kara da cewa, “har yanzu dai ana ci gaba da bincike, kuma sai ƙarin haske ake samu. Saboda haka muna kira ga jama’a su yi watsi da duk wasu surutai da ba su ji daga bakin EFCC ɗin ba.”

Haka sanarwar ta ƙunsa, wadda aka fitar da ita a ranar Asabar, mai ɗauke da sa hannun Kakakin EFCC, Dele Oyewale ya sa wa hannu.

Tsohuwar Minista Sadiya Farouq da dakatacciyar Minista, Betta Edu har yanzu su na fuskantar bincike, ba a tantance su ba.

Sadiya ta yi Minista a ƙarƙashin tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kuma EFCC na binciken ta dangane da wata saɓat-ta-juyattar Naira biliyan 37.1, waɗanda kuɗaɗe ne na tallafin marasa galihu.

Cikin watan Janairu Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Minista Betta Edu, wadda ta gaji Sadiya, bayan an fallasa wata takardar da ta nuna yadda aka wafci wasu kuɗaɗen tallafin marasa galihu ba bisa ƙa’ida ba.

Bayan an shafe watanni tun bayan fara binciken su, jin an yi shiru dangane da batun su, dai aka fara raɗe-raɗin cewa EFCC ta wanke su, kuma an binne harƙallar, an manta da batun.

Ko kwanan nan lauyan Edu ya aika wa BBC wasiƙar barazanar maka su kotu, saboda zargin sun ɓata mata suna.

To sai da EFCC ta ce ba ta wanke kowa ba, kuma ba a binne harƙallar ba.

Maimakon haka, EFCC ta ce an ma faɗaɗa bincike ne, kuma yanzu haka an ma dakatar da wasu ma’aikatan hukumar da dama.