Ɗalibai 1,680 aka sace a shekaru 10 a Nijeriya — UNICEF

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya ce hare-hare da sace-sacen da ake kai wa ‘yan makaranta a Nijeriya ya karu tun bayan sace ‘yan matan makarantar Chibok a jihar Borno shekaru 10 da suka gabata.

UNICEF, a cikin wani rahoto da ta fitar a jiya Litinin, ta ce kashi 37 na makarantu a jihohi 10 ne kawai ke da tsarin gargaɗin farko na gano barazanar irin waɗannan hare-hare.

Rahoton ya yi la’akari da alƙaluma masu ban tsoro na tashe-tashen hankula da suka shafi yara.

A cikin shekaru 10 da suka gabata, an sace yara fiye da 1,680, an kashe 180 a hare-haren makarantu, sannan an yi garkuwa da ma’aikatan makarantar 60 tare da kashe 14.

Bugu da ƙari, an kai hare-hare sama da 70 a makarantu, inji rahoton.

UNICEF ta kuma jaddada cewa har yanzu akwai ‘yan matan makarantar da aka sace su 90, kuma a baya-bayan nan ƙasar ta sake fuskantar wani garkuwa da ɗalibai a jihar Kaduna a watan Maris.

UNICEF ta yi kira ga hukumomi da su ƙara ƙaimi wajen kare yara masu rauni da inganta matakan tsaro a makarantu.

Wakiliyar UNICEF a Nijeriya, Ms. Cristian Munduate, ta bayyana buƙatar magance musabbabin rikicin, inda ta jaddada cewa ilimi wani muhimmin haƙƙi ne ga makomar yara da kuma kawar da talauci.