Gwamnatin Nijeriya na biyan tallafin mai a yanzu fiye da a baya – El Rufa’i

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufai ya yi zargin cewa gwamnatin Nijeriya na ci gaba da biyan tallafin mai wani abu da ya ce an Nijeriya da dama ba su sani ba.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, El Rufai ya ce a yanzu gwamnati na biyan fiye da abin da take biya a matsayin tallafin mai a baya.

Ya bayyana cewa matakai da dama da aka tanada na rage raɗaɗin janye tallafin mai ba sa tasiri abin da a cewarsa ya sa aka maido da tsarin.

A jawabin da ya yi lokacin da ya sha rantsuwar kama aiki, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin mai.

Sai dai El Rufai wanda a lokacin ya nuna goyon baya ga tsarin, ya ce dole ta sa gwamnatin yin gyare-gyare.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito El Rufai na cewa wurin aiwatar da tsarin, kamar yadda ake gani, gwamnatin a yanzu ta gano cewa dole a ci gaba da biyan tallafin, muna biyan kuɗi mai yawa kan tallafi fiye da yadda take biya a baya.

“Dalilin shi ne saboda an ga tasirin hakan sannan tsare-tsaren da aka shirya domin rage tasirin cire tallafin ba su yi wani tasiri ba, a don haka gwamnatin tarayya ta koma biyan tallafin mai.”

Ya ce mutane da dama ba su san cewa gwamnati tana ci gaba da biyan tallafin mai ba, “amma idan suna son su san ko ana biya ko a a, su duba farashin mai da dizel saboda kamata ya yi mai ya fi tsada a kan dizel amma farashin dizel ya haura naira dubu ɗaya yayin da man fetur yake kan naira 600 duk lita guda.

“Don haka, har yanzu muna biyan tallafin mai saboda gwamnati ta gane cewa yadda ta aiwatar da tsarin biyan tallafin tun farko na buƙatar a sake nazari a kai,” inji shi.