Jami’an tsaro sun hana ’yan majalisar dokoki shiga fadar Sarkin Dutse wajen naɗin Sardauna

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Jami’an tsaron farin kaya sun hana Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Alhaji Lawan Muhd Dansure, shiga fadar Mai Martabar Sarkin Dutse a lokacin bikin naɗin Sardaunan Dutse, Alhaji Nasiru Haladu Dano, wanda ya gaji kujerar Marigayi Alhaji Bello Maitama Yusuf, tsohon Sardaunan Dutse, wanda ya rasu a shekarar da ta gabata. 

Jami’an tsaron sanye da baƙaƙen gilasai sun samu damar korar Shugaban Masu Rinjaye da tawagarsa ne a lokacin da su ka halarci fadar ta Mai martaba Sarkin na Dutse, Alhaji Hamim Muhd Sunusi, a lokacin da ya ƙaddamar da naxin Alhaji Nasiru Haladu Dano a matsayin sabon Sardaunan na Dutse. 

Hana Shugaban Masu Rinjayen shiga fadar ya ɓata wa mutane da dama rai ciki harda sauran ‘yan majalisar dake cikin tawagarsa da sauran jama’a da suke ƙofar shiga wurin da ake gudanar da naɗin, lamarin da ya sa ‘yan majalisar suka fice daga fadar cikin fushi suka hau doguwar motarsu suka fice daga fadar suka koma inda suka fito.

Daga cikin waɗanda suka rufawa Shugaban Masu Rinjayen baya a majalisar jihar sun haɗa da Alh Aminu Sule Sankara da Yahaya Muhd Maliya da Ilu Maku Garki da Ibrahim Hamisu Kanya da  Aminu Zakari Tsubut a lokacin da suka rufawa Alh Lawan Muhd Dansure baya domin zuwa fadar domin ganin yadda naɗin yake gudana.

Jami’an tsaron ba su tsaya iyakan ‘yan majalisar ba hatta sakataren mai martaba Sarkin Alh Wada Alh bai tsira ba sai da suka yi iya ƙoƙarinsu wajen hana sakataren shiga fadar wurin da ake gudanar da naɗin sai da wasu manema labarai suka gaya masu cewa shine sakataren Sarki sannan suka bar shi ya shiga saboda ba su san shi ba.

Yayin da ‘yan jaridu da dama katin shaidarsu bai yi masu amfani ba wajen shigar fadar inda ake bikin naxin domin jami’an tsaron sun ƙi barinsu su shiga.

Yayin da mutane da dama ciki har da wasu daga cikin shugabannin ƙananan hukumomi ba su samu ikon shiga ɗakin taron ba saboda barazanar jami’an tsaro da kaucewa cin zarafinsu yayin da mawaƙa da dogarai da makaɗa aka yi fatali da su gefe ɗaya aka hanasu shiga suma.

A ɓangare ɗaya kuma ‘yan sane ne suka ci karensu babu babbaka wajen sanyawa mutane hannu a aljihu suna ɗauke masu ‘yan kuɗaɗe da wayoyi a lokacin fitowa da lokacin shiga wajen taron naɗin saboda kokawa.

Duk da hakataron naɗin ya sami halartar tsohon shugaban ƙasa Janar Muhammadu Buhari da Mataimakin Shugaban Ƙasa Ƙashim Shrttima da Janar Burtai da sanatoci da manyan ministocin ƙasar nan har ma da baƙi daga ƙasashen waje.

An yi wa fadar ta Dutse kwalliya ta musamman saboda da gagarimin naɗin yayin da kowa ka duba a fada da kewaye yana cikin farin ciki saboda yadda bikin ya ƙayatar.