‘Yan bindiga sun kashe basarake a Taraba

Daga BASHIR ISAH

‘Yan bindiga a Jihar Taraba sun kai hari tare da kashe sarkin masarautar Sansani, Alhaji Abdulmutalib Jankada, da ke cikin Ƙaramar Hukumar Gassol a jihar.

Majiyoyi sun ce maharan sun shiga ƙauyen Sensani ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 9 na dare inda suka tafi kai tsaye zuwa fadar masarautar ƙauyen sannan suka kashe Nuhu a gidansa da ke kusa da Ibbi.

Majiyarmu ta ce za a yi jana’izar marigayin bayan an sauka daga Sallar Juma’a daidai da karantarwar Musulunci.

Ya zuwa haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga ɓangaren hukuma kan batun.