Ƙarancin kayan aiki ya addabi makarantun Jihar Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Ƙaran cin kayan koyarwa ya addabi makarantu da malamai a Jihar Jigawa, lamarin da ya sa wasu daga cikin malaman makarantun Jihar gabatar da ƙorafin su ga manema labarai.

Kaɗan daga cikin ƙorafin ya haɗa da ƙarancin alli da rijistar ɗalibai da tsarin karantawar, wato scheme of work da kuma ƙarancin littatafan karatu.

A hannu guda malaman sun yi ƙorafin rashin kulawa a kansu wajan ƙarin girma da gazawar gwamnati wajen biyansu haƙƙinsu na ƙarin girma a kan lokaci.

Masu ƙorafin waɗanda suka buƙaci a sakaya sunansu, sun ce ce da yawa daga cikinsu da aka ƙara girma a bakin aiki har yanzu albashinsu bai sauyaba, wato dai ga girma a takarda amma babu shi a aikace.

Don haka suka buƙaci gwamnatin Jihar Jigawa ta duba matsalarsu, kuma maimakon a ce gwamnatin tana kula da haƙƙinsu sai ƙara jibga musu matsaloli take yi.

Haka nan, sun koka kan cewar an shigo da wani sabon tsari na cewa dole malamai su koma bakin aikin kafin dawowar ɗalibai da sati ɗaya bayan kammala hutu, alhali gwamnatin jihar ba ta kula da haƙƙin malamai yadda ya kamata.