13
Jan
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Pindiga, ita ce helikwatar mulkin masarautar Pindiga, wacce kuma ɗaya ce daga cikin masarautun Jihar Gombe. Wannan gari mai daɗaɗɗen tarihi, Jukunawa suka kafa shi a tsakankanin ƙarni na goma sha shida zuwa ƙarni na goma sha bakwai. Garin ya fara daga ɗan ƙaramin matsugunni na wasu jama’a a kan dutse har zuwa bunƙasarsa kamar yadda yake a yau a matsayin masarautar sarkin yanka mai daraja ta biyu a cikin Jihar Gombe. Asali: Pindiga, gari ne mai tsohon tarihi, asalin kafuwar wannan gari yana farawa daga lokacin da Jukunawa suka shigo yankunan baƙaƙe daga ƙasar Yamen,…