Musulmi sun yi azumi cikin zafin rana da na aljihu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A yayin da nake wannan rubutu ya rage saura kwanaki ƙalilan musulmi su kammala azumin watan Ramadan na 2024, kamar yadda suka saba gudanarwa duk shekara har tsawon kwanaki 30 ko 29. Sai dai a bana an gudanar da azumin ne cikin wani yanayi na tsananin zafin rana, wanda a wasu ranakun har yana kai digiri 38 zuwa 40 na ma’aunin zafi a Nijeriya. Hakan ya jefa mutane da dama cikin wani muwuyacin hali, a yayin da suke ƙoƙarin sauke haƙmin ibada na wajibi da ke kansu.

Kamar yadda muka sani, azumi wani muhimmin rukuni ne cikin shika-shikan Musulunci guda biyar, wanda yake mataki na huɗu. Musulmi na barin ci da sha da kusantar iyali ne na tsawon wuni guda, daga fitowar rana zuwa faɗuwarta, lokacin da za su ajiye azumin su yi buɗe-baki, kafin su sake ɗaukar wani. Ana wannan azumi ne domin samun tsarkin zuciya da kusantar ubangiji, inda Musulmi masu azumi ke shagaltuwa da ayyukan ibada iri-iri da suka haɗa da karatun Alqur’ani Mai Girma, sallolin nafila, da zikirori na neman gafara daga zunubai.

Nijeriya na daga cikin ƙasashen Afirka irinsu Mali, Senegal, Mauritania, Djibouti, Gambia, Nijar, da Sudan ta Kudu, waɗanda ke fama da matsalar tsananin zafin rana da fari, da rashin wadatar abinci, sakamakon kwararar hamada, kuma akasarin mutanen waɗannan ƙasashe musulmi ne da su ma suka gudanar da wannan azumi na ibada.

A Nijeriya, Musulmi a jihohi irinsu Borno, Yobe, Adamawa, Kano, Katsina, Sakkwato, Oyo, da Oshun, sun fuskanci tsananin zafi sosai, wanda ya sa mutane da dama yin azumin cikin matsanancin wuya, wasu ma sun ajiye azumin zuwa wani lokaci nan gaba, bayan yanayi ya yi sanyi, saboda lalura ta rashin lafiya. Mun ga yadda wasu ke yawaita wanka da ruwan sanyi akai-akai, ko wanke kansu da ruwan sanyi, don samun sassauci daga zafin da ke addabarsu.

Farfesa Charles Anosike, Shugaban Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Nijeriya (NiMet) ya bayyana hasashen da hukumarsa ta yi cewa, a bana za a fuskanci tsananin zafin rana fiye da wanda aka fuskanta a baya. Sannan wani rahoton Ƙungiyar Kula da Yanayin Muhalli ta Duniya (World Weather Attribution) ya bayyana cewa tun a watan Fabarairu na wannan shekara wasu ƙasashen Afirka ta Yamma suka fara fuskantar tsananin zafi da suka haɗa da Nijeriya, Benin, Togo, Ghana, Cote d’Ivoire, Liberiya, Sierra Leone, da kuma wasu yankuna na Gini da Kamaru.

A wani bayani da ya fitar game da tsananin zafin da ake fuskanta, Wasiu Adeniyi Ibrahim, shugaban ofishin kula da hasashen yanayi na Hukumar NiMet, ya bayyana fargabar za a iya fuskantar tsananin zafi nan gaba fiye da wanda ake gani yanzu a wasu ƙasashen yankin Afirka ta Yamma, sakamakon yadda yanayin ke ƙara zafafa a kowacce rana.

Wannan ya tabbatar da cewa tun kafin watan Ramadan ya kama akwai bayanai da ke nuna za a yi azumi cikin ƙunci da yanayin zafi. Don haka akwai buƙatar samar da matakan rigakafi da nufin rage ƙuncin da za a iya fuskanta. Sai dai mu malamanmu da ’yan bokonmu ba su cika damuwa da rahoton hasashen yanayi ba, ballantana ma har a sanar da jama’a su fahimci yadda za su samu sauƙin yin azumi cikin yanayin tsananin zafi.

Sai a kafafen watsa labarai na ƙasashen waje irinsu BBC Hausa, TRT Afirka da DW aka riƙa ganin bayanai na faɗakarwa ga masu azumi yadda za su kula da kansu a wannan yanayi. Shafin yanar gizo na BBC Hausa ya bayyana wasu dalilai da suka haifar da wannan tsananin zafi da suka haɗa da juyawar ruwan teku mai ɗumama, sauyin yanayi, cunkushewar birane, da yawan sare itatuwa, har ma da sauyi wajen tsarin muhalli.

Sannan BBC Hausa ta kuma bayyana wasu daga cikin illolin da wannan tsananin zafi zai iya haifarwa da suka haɗa da sanya mutane cikin ƙunci da yawan jin zafi ko fitar da zufa, tsananta lalurar masu ciwon suga da na zuciya da ƙoda. Yana kuma janyo katsewar wutar lantarki da gazawar injuna. Wannan ya nuna mana irin abubuwan da mutane za su yi fama da shi cikin wannan yanayi na zafi da ake ciki.

Ba ma batun zafin rana da ake ganin canjin yanayi ne ya haifar da shi ba, hatta batun tashin farashin kayan masarufi da tsadar kayan abinci a kasuwanni da kantuna ya sa azumin bana ya zo wa Musulmi cikin mawuyacin yanayi. Rana zafi inuwa ƙuna kenan in ji masu azancin magana. Sai dai duk da haka za a iya cewa sambarka domin kuwa ba kamar yadda aka za ta ba, gwamnati, ’yan siyasa da masu hannu da shuni, kamfanoni da ƙungiyoyi masu zaman kansu sun taimaka sosai wajen rabon kayan abinci ga mabuƙata, a wasu wuraren ma har da rabon dafaffen abincin buɗe-baki aka riqa rabawa ga jama’a, duk domin a samu sassauci daga wahalhalun da jama’a ke fuskanta na halin talauci da yunwa, sakamakon yanayin da tattalin arzikin ƙasa ke ciki.

Sai dai duk da haka a wasu wurare canjin yanayi ya haifar da ƙarancin ruwan sha da na aikin gida, ga kuma ƙarancin wutar lantarki wanda ya sa ko da ruwan leda mutum zai saya, sai dai ya yi haƙuri ya saya da tsada saboda yadda farashin ruwa mai sanyi da aka fi buƙata ya ninka marar sanyi. Haka su ma masu sayar da ƙanƙara sun ƙara farashi cikin azumi, saboda a cewarsu rashin samun wutar lantarki akai-akai ya sa suke amfani da janareto wanda shi kuma yake amfani da man fetur. Kowa yanzu ya san yadda farashin litar mai yake ko da a gidan man ne ballantana kuma a wajen ’yan bunburutu!

A Jos, sai da ta kai wata ƙungiya ta sayi motar tankar ruwa ta riƙa bi anguwa-anguwa tana raba wa mutane ruwa, don su samu damar yin ibada da ayyukan gida, tsananin wahalar ruwa da ake fuskanta, da kuma tsadar wanda ake sayarwa. Wanda shi ma ake dangantawa da rashin wutar lantarki, sauyin yanayi. Garin da a shekarun baya aka fi sani da yanayi mai sanyi da daxin zama, yanzu shi ma ya koma kamar yanayin jihohin da ke maƙwaftaka da garin, irinsu Bauchi da Kaduna.

Sai dai masana harkokin kiwon lafiya, sun shawarci jama’a, musamman masu azumi a wannan lokaci su riqa yawan shan ruwa bayan buxa baki har zuwa lokacin sahur, da shan ’ya’yan itace na marmari, da kuma rage yawan shiga rana in ba ta kama dole ba, da kuma sa kaya marasa nauyi don rage yawan zufa. Waɗannan na daga cikin abubuwan da za su taimaka masa wajen samun sauƙin wahalar azumi da zai iya fuskanta saboda tsananin zafin rana.

Sannan ko da ba a azumi ba, yana da muhimmanci jama’a su riƙa shawartar masana kiwon lafiya da masu hasashen yanayin muhalli, domin sanin me ya kamata su yi don fuskantar sauyin yanayi da zafin rana da za su iya shiga, domin kare lafiyarsu da halittarsu.